Connect with us

News

Kotun sauraren kararrakin zabe Ta Sauke Wani Sanata Daga Kujerarsa

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

Kotun sauraren kararrakin zabe dake zamanta a birnin Lokoja, Ta sauke shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da aiyukan hukumar hana fasa kwauri ta kasa, Sanata Jibrin Isah daga kan kujerarsa ta sanata, Bayan data soke sakamakon zabe na rumfunan zabe 94 da suke a shiyyar da yake wakilta.

A yanzu haka mai shari’a K.A Orjiako, Ya umarci hukumar zabe ta kasa ta gaggauta janye shaidar cin zabe data baiwa sanatan, Sannan ta sake gudanar da zaben cike gibi a rumfunan zabe da abun ya shafa.

UNICEF Za Ta Samar da Ginin Ma’aunin Harhada Adana a Jihar Kano

Dan takarar jam’iyyar PDP, Dr Victor Adoji ne ya shigar da kara gaban kotun, inda yake kalubalantar nasarar da Sanata Isah ya samu, bisa ikirarin cewar an soke sakamakon zabe a wasu akwatinan zabe da aka samu aringizon masu kada kuri’a.

A hukuncin da alkalin kotun ya yanke ya amince da dukkanin wasu shaidu da mai kara ya shigar gaban kotun.
Sanata Isa dan shekara 63 a duniya ya kasance tsohon dan siyasa, Kuma shine wanda aka gani ya durkusawa Gwamna Yahya Bello na jihar Kogi ya bashi hakuri, kamar yadda aka nadi bidiyon nasa ta cikin wata kyamara.

UNICEF Za Ta Samar da Ginin Ma’aunin Harhada Adana a Jihar Kano

A wani labarin kuma Gwamnatin tarayya ta ce ana shirin yin garambawul ga shirin N-Power domin daukar karin masu amfana da kuma tabbatar da biyan alawus ba tare da bata lokaci ba.

 

Shirin na N-Power wani shiri ne da ke da nufin bunkasa fasahar matasa da bunkasa harkokin kasuwanci.

 

Ministar jin kai da kawar da fatara, Betta Edu ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi a Abuja.

 

Ministar ta ce za a sake kaddamar da shirin tare da sabon tsari da kumakudiri.

 

Ta ce ma’aikatar na shirin kafa cibiyoyin jin kai a fadin kananan hukumomi 774 a matsayin wani dogon buri na kawar da talauci a kasarnan.

 

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement