Connect with us

News

Kungiyar kwadago ta Kasa NLC ta sanar da kawo karshen yajin aikin gargadi na kwanaki biyu.

Published

on

Kungiyar kwadago ta Kasa NLC na zanga zanga

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Kungiyar kwadago ta Kasa NLC ta sanar da kawo karshen yajin aikin gargadi na kwanaki biyu.

Yanzu haka kungiyar ta umarci mambobinta a duk fadin kasar da su koma bakin aiki.

A wata sanarwa da shugaban Kungiyar Joe Ajaero, ya fitar a Daren Laraba ya ce, an samu gagarumin ci gaba a yajin aikin kwana ki Biyu da kungiyar ta yi.

Kotun sauraren kararrakin zabe Ta Sauke Wani Sanata Daga Kujerarsa

A ranakun Talata da Laraba ne kungiyar kwadago ta shiga yajin aikin kwanaki biyu a fadin kasar, sakamakon rashin cika yarjejeniyoyin da gwamnatin tarayya ta kulla na cire tallafin man fetur.

Matakin da ma’aikatan NLC suka dauka ya sa wasu sun fara tunanin gur-gunta harkokin tattalin Ar-ziki da kasuwanci a jihohi da dama da yajin aikin ha haifar.

Mun yi farin cikin bayar da rahoton cewa, albarkacin jajircewar da kuka yi, mun samu gagarumar nasara wajen cimma manufofin da aka sanya a gaba a taron majalisar zartarwa ta kasa (NEC), wanda ya sa aka fara wannan yajin aikin gargadi,” in ji Ajaero.

“A bayyane yake cewa saƙonmu na haɗin kai ya bi sahun gwamnati da babbar murya, kuma zai sa a ɗauke shi da muhimmanci.

“Yayin da muke kawo karshen yajin aikin gargadi na kwanaki biyu a fadin kasar a yau, da tsakar dare, muna kira ga dukkan ku da ku kammala yajin aikin cikin alheri, mu koma bakin aiki gobe, bisa ga yarjejeniyar farko da muka kulla.

Wani labarin kuma Kotun sauraren kararrakin zabe Ta Sauke Wani Sanata Daga Kujerarsa

Rashin wutar lantarki da ake fama dashi tun kafin yanzu ya kara tsananta jiya a nan Jihar Kano, A yayin da kanfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO ya tsayar da aiyukansa kacokan, Lamarin da ya haifar da daukewar lantarki baki daya a cikin birnin Kano.

Wata sanarwa da shugaban sashin sadarwar kanfanin, Sani Bala Sani ya fitar, Ya alakanta daukewar wutar lantarkin da yin biyayya ga umarnin kungiyar kwadago ta kasa na tafiya yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyu.

Sanarwar da aka wallafa a shafin X na kanfanin, Ta baiyana cewar za’a cigaba da fuskantar matsalar daukewar wutar lantarkin, kasancewar yajin aikin gargadin zai ci gaba da kasancewa a yau Laraba.

Shima mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Kano, Kwamared Ado Riruwai, ya tabbatar da cewar kungiyarsu ta rufe dukkanin wasu ofisoshin gwamnati dake jihar Kano, domin tabbatar da yajin aikin gargadin.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement