Connect with us

Sport

Babu sauran adawa tsakanina da Messi – Cristiano Ronaldo

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Fitaccen ɗan ƙwallon duniya Cristiano Ronaldo ya ce shi da babban abokin hamayyarsa a fagen ƙwallon ƙafa, Lionel Messi “sun sauya tarihin ƙwallon ƙafar duniya”, to sai dai ya ce yanzu adawa tsakaninsu ta ‘wuce’.

‘Yan wasan biyu – da ake yi wa laƙabi da, ‘yan wasan da suka fi shahara a tarihi, ‘Gaot’ – sun sha fuskantar juna a lokacin da suke buga gasar La Liga a ƙungiyoyin Real Madrid da Barcelona.

Advertisement

Majalisar Wakilai Ta Sha Alwashin Fallasa Masu Satar Man Fetur a Najeriya

“Dukkanmu ana girmama mu a duniya, wannan shi ne babban abu mafi muhimmanci”, in ji Ronaldo.

Ronaldo – wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau biyar – a bana baya cikin mutanenda ke takarar kyautar karon farko tun 2003, yayin da Messi zai iya lashe kyautar karo takwas a tarihi.

“Ya kafa tarihi, ni ma na kafa nawa, ya yi abin da ya dace, daga abin da na gani,” in ji Ronaldo mai shekara 38 da a yanzu ke taka leda a ƙungiyar Al-Nassr ta Saudiyya.

Advertisement

Yayin da aka tambaye shi game da cewa shin ƙiyayya na daga cikin adawarsu?, sai ya ce “bai kamata waɗanda ke son Ronaldo, su ƙi Messi ba, bana kallon adawa a haka”.

“A yanzu adawa ta ƙare, mun shafe shekara 15 muna jan zare a harkar ƙwallon ƙafa, don haka yanzu mun wuce abokai, mun zaman ƙwararrun abokan sana’a, kuma muna girmama junanmu”.

‘Yan wasan sun cimma nasarori masu yawa a fagen wasan ƙwallon ƙafa, inda suka lashe kyaututtuka masu ɗimbin yawa a harƙar ƙwallon ƙafa.

Advertisement

Ronaldo shi ne ɗan wasan da ya fi kowa zira ƙwallaye a Real Madrid inda ya ci 451 a wasa 438 da ya yi wa ƙungiyar, tare da cin kofuna 16 ciki har da Kofin Champions Leagues huɗu da na La Liga biyu da na Copas del Rey biyu a tsowan shekara tara da ya yi a Bernabeu.

Shi kuwa Messi – wanda a yanzu ke wasa Inter Miami ta Amurka – ya kasance ɗan wasan da ya fi ci wa Barcelona ƙwallaye inda ya ci 674 a wasa 781 da ya buga wa ƙungiyar.

Messi – mai shekara 36 ya lashe kofuna 35 a Barcelona, ciki har da kofin La Liga 10 da kofin Champions League hudu da Copa del Rey bakwai.

Advertisement

A matakin ƙasa kuwa Messi ya taimaka wa Argentina lashe Kofin Duniya da aka buga a Qatar a 2022, sannan ya ɗauki kofin Copa America, yayin da shi kuma Ronaldo ya taimaka wa Portugal ɗaukar kofin nahiyar Turai da kofin ‘Nations League’.

‘Yan wasan sun fuskanci juna a fili sau 36, haɗuwarsu ta ƙarshe shi ne a watan Janairu a lokacin da ƙungiyar Messi ta PSG ta doke ta Al-Nassr da ci 5-4 a wasan sada zumunta.

Advertisement
Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *