Connect with us

Business

Kanfanonin Kasar Indiya Zasu Zuba Jarin Dala Bilyan 14 A Najeriya

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Ziyarar da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya kai kasar Indiya ta fara haifar da ‘Da mai ido, A yayin da tun kafin dawowar shugaban kasar gida, wasu Kanfanonin Indiya guda hudu suka yi alkawarin zuba jarin Dala Bilyan 14 a kasar nan.

Kanfanonin sun hada Indorama Petrochemical Limited da Kanfanin sarrafa karafa da samar da lantarki na Jindal Steeel anda Power Limited.

Victor Oshimhen Ya Shiga Cikin Jerin masun neman kyautar Ballon d’Or

An kulla yarjejeniyar zuba jarin ne a yayin wata ganawa da aka yi tsakanin masu kanfanonin da shugaban kasa a ranar Laraba, kamar yadda yake kunshe a wata sanarwa da kakakinsa Ajuri Ngelale ya fitar.
Bola Tinubu ya yabawa kanfanonin tare da bawa ‘yan kasashen waje masu sha’awar zuba jari a kasar nan tabbacin samun riba mai ma’ana a kasuwancinsu.
A yanzu haka dai shugaban kasar na a birnin New Delhi, Inda yake halatar taron kungiyar kasashe ta G20 wanda za’a gabatar daga ranar 9 zuwa 10 ga watan da muke ciki na Satumba.

Victor Oshimhen Ya Shiga Cikin Jerin masun neman kyautar Ballon d’Or

Wani labarin kuma Rashin wutar lantarki da ake fama dashi tun kafin yanzu ya kara tsananta jiya a nan Jihar Kano, A yayin da kanfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO ya tsayar da aiyukansa kacokan, Lamarin da ya haifar da daukewar lantarki baki daya a cikin birnin Kano.

Wata sanarwa da shugaban sashin sadarwar kanfanin, Sani Bala Sani ya fitar, Ya alakanta daukewar wutar lantarkin da yin biyayya ga umarnin kungiyar kwadago ta kasa na tafiya yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyu.
Sanarwar da aka wallafa a shafin X na kanfanin, Ta baiyana cewar za’a cigaba da fuskantar matsalar daukewar wutar lantarkin, kasancewar yajin aikin gargadin zai ci gaba da kasancewa a yau Laraba.

Shima mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Kano, Kwamared Ado Riruwai, ya tabbatar da cewar kungiyarsu ta rufe dukkanin wasu ofisoshin gwamnati dake jihar Kano, domin tabbatar da yajin aikin gargadin.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement