Connect with us

News

PDP:Za mu dauki mataki na gaba kan hukuncin Kotun Sauraron Karar Zabe 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta yi watsi da hukuncin da Kotun Sauraron Kararrakin Zabe ta yanke na tabbatar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasa.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba da daddare bayan yanke hukuncin, mai dauke da sa hannun sakataren watsa labaranta Debo Ologunagba, PDP ta ce ta yi nazari kan hukuncin kuma ba ta yarda da shi ba dungurungum.

Akwai Yiwuwar Samun Mamakon Ruwan Sama Kamar Da Bakin Kwarya Nan Da Kwanaki 3 Masu Zuwa-NIMET

A ranar Laraba ne kotun ta yi zamanta na karshe don yanke hukunci a kan kararrakin da jam’iyyun PDP da na LP suka yi suna kalubalantar nasarar Bola Tinubu, inda aka shafe awa kusan 12 ana yanke hukuncin.

“Hukuncin ya ci karo da dalili da hujjoji da shaidun da aka gabatar a kotu, ya ci karo da Dokokin Zabe da Tsare-Tsare da Hurumi da ma Kundin Tarin Mulkin Nijeriya na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima).

“Hakika hukuncin yana cike da kura-kurai kuma lokacin ya yi gajarta wajen yanke cikakken hukunci kan batun,” in ji jam’iyyar.
PDP ta kara da cewa a matsayinta na jam’iyya mai bin dokar kasa, tuni ita da lauyoyinta suka yi wa hukuncin kyakkyawan nazari tare da daukar mataki na gaba da ya dace bisa dokar shari’a.

Sannan a karshe ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su kwantar da hankulansu “a yayin da jam’iyyarmu za ta ci gaba da jagorantar kare dimokuradiyya don tabbatar da cika muradun mutane kamar yadda suka nuna a zaben shugaban kasa na 25 ga watan Fabrairun 2023,” sanarwar ta ce.

Mene ne korafe-korafen Atiku Abubakar da kotun ta watsar?

Kotun Sauraron Kararrakin Zaben ta yi watsi da korafin Atiku Abubakar da ya nemi a soke sakamakon zaben shugaban kasa na jihohin Kano da Legas.

Kotun ta ce masu korafin ba su hada da Peter Obi da Rabiu Kwankwanso ba wadanda suka samu kuri’u mafi yawa a jihohin biyu.

Kotun ta kuma yi watsi da korafin Atiku Abubakar da na jam’iyyarsa ta PDP kan zargin cewa Shugaba Tinubu yana da takardar shaidar zama dan kasashe biyu da kuma na zargin tuhumarsa da safarar kwaya.

Sai kuma Mai Shari’a Moses Ugo shi ma ya yi watsi da karar da ya karanto kan batun rashin cancantar Tinubu saboda rashin shaidar karatu, inda ya ce wannan sabuwar kara ce, kuma ba zai yiwu Atiku da PDP su shigar da sabon korafin da tun farko ba su gabatar da shi ba.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement