Connect with us

News

Wasu masu garkuwa da mutane suka yi garkuwa da mutane 19 a A Abuja

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

A ranar Alhamis wasu masu garkuwa da mutane suka yi garkuwa da mutane 19 a yankin Bwari da ke cikin babban birnin tarayya Abuja.

Rahotanni na  zuwa ne kasa da ‘yan kwanaki da mutuwar mutum 30 a sakamakon ruftawar masu hakar ma’adinai ta zama sababi a yankin Kuje da ke cikin birnin tarayya Abuja.

Advertisement

Wasu Sun Bayyana Cewa Barace-Barace Suke Rayuwa Saboda Tsananin Yunwa

Ministan babban birnin tarayya l, Nyesom Wike, shi ne ya shaida hakan a lokacin da ke ganawa da shugabannin yankuna shida na Abuja.

Haka kuma Ministan Nyesom Wikewanda ya nuna mamakinsa da matakin, ya ce, zai gayyaci daraktan hukumar tsaron farin kaya na FCT, kwamishinan ‘yansanda don samun cikakken bayani game da garkuwar da kuma matakan da za a bi wajen kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su din.

Wike ya bukaci shugabannin tsaro da suka samar da ‘yan sintiri a yankunan don su ke bibiyar ayyukan masu hakar ma’adinai, ya kara da cewa zai gana tare da takwaransa na ma’aikatar albarkatun kasa, Dele Alake, domin dakile hakar ma’adinai ta barauniyar hanya a birnin tarayya.

Advertisement

Kazalika, karamar ministan birnin tarayya Abuja, Dakta Mariya Mahmoud, da babban sakataren hukumar bunkasa shiyyar birnin tarayya FCTA, Mr Olusade Adesola, sun nuna kwarin guiwarsu kan hukumar kula da birnin tarayya Abuja.

Da yake magana kan matsalolin da yankin Kwari ke fuskanta, shugaban yankin, Danladi Chiya, ya roki ministan da karamin ministan birnin tarayyar da su zo domin taimaka musu.

Haka kuma “Tun lokacin da muka ji labarin nadinku, muka ji dadi da fatan cewa matsaloli za su zo karshe.”

Advertisement

Haka zalika yace “Babban matsalarmu da ke fuskantar dukkanin yankunan shida na Abuja shi ne matsalar tsaro. Ko a yau (Alhamis) mutum 19 aka yi garkuwa da su a yankin Bwari. Yanzu nake samun labarin cewa mutanen yankin sun fi kwanaki shida a hannun masu garkuwa.”

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *