Connect with us

News

Wasu Sun Bayyana Cewa Barace-Barace Suke Rayuwa Saboda Tsananin Yunwa

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Al’ummar wasu yankunan Zamfara da matsalar tsaro ke daɗa rincaɓewa sun ce da dusa da kuma barace-barace suke rayuwa saboda tsananin yunwa.

Advertisement

Rahotanni na bayyana cewa a yanayin da ake ciki a yanzu, matsalar tsaro ta kai bango a Wanke da Magami da ‘Yar Tasha da Ɗan Sadau da Ɗan Kurmi da dai sauran sassa na jiha.

BUDADDIYAR WASIKA ZUWA MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR KANO ENG. ABBA KABIR YUSUF

Kuma galibin mazauna waɗannan ƙauyuka na cewa suna cikin wani hali irin na ni-‘ya-su saboda azaba da hana su sakat da ‘yan bindiga ke yi.

Tsawon sama da shekara goma kenan, mazauna sassan jihar Zamfara, na fama da hare-haren ‘yan fashin daji waɗanda suke auka wa ƙauyuka da garuruwa, inda suke kashe-kashe da jikkata mutane, tare da sace wasu don neman kuɗin fansa daga danginsu.

Advertisement

Wani magidanci da BBC ta tattauna da shi ya ce ”Ba ka isa ka taso daga Gusau ka nufi Magami ba, idan babu rakiyar ‘yan sa-kai ko sojoji.

Rashin fita gonaki da ‘yancin noma, na cikin abubuwan da suka sake kassara mutane yankunan da ma ƙauyukansu.
Monaman da BBC ta tattauna da su, na cewa ba su da ikon yin tafiyar kilomita guda daga garin Magami, sai an sace mutum ko a harbe shi. Manomin ya ce a halin yanzu haka mata da yawa sakin aurensu ake yi saboda rashin abinci,

Wani labarin kuma BUDADDIYAR WASIKA ZUWA MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR KANO ENG. ABBA KABIR YUSUF

Advertisement

Rashin wutar lantarki da ake fama dashi tun kafin yanzu ya kara tsananta jiya a nan Jihar Kano, A yayin da kanfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO ya tsayar da aiyukansa kacokan, Lamarin da ya haifar da daukewar lantarki baki daya a cikin birnin Kano.

 

Wata sanarwa da shugaban sashin sadarwar kanfanin, Sani Bala Sani ya fitar, Ya alakanta daukewar wutar lantarkin da yin biyayya ga umarnin kungiyar kwadago ta kasa na tafiya yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyu.

Advertisement

 

Sanarwar da aka wallafa a shafin X na kanfanin, Ta baiyana cewar za’a cigaba da fuskantar matsalar daukewar wutar lantarkin, kasancewar yajin aikin gargadin zai ci gaba da kasancewa a yau Laraba.

Shima mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Kano, Kwamared Ado Riruwai, ya tabbatar da cewar kungiyarsu ta rufe dukkanin wasu ofisoshin gwamnati dake jihar Kano, domin tabbatar da yajin aikin gargadin.

Advertisement
Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *