Connect with us

News

Sabuwar Hanyar Kwacen Shafin Facebook

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI. 

A kwanan nan kwacen shafin sada zumunta na Facebook wanda a turance ake kira ‘Hacking’ ya zama ruwan dare, mafi yawan mutane sun rasa ta yaya hakan yake faruwa.

To yanzu za mu dan yi bayanin yadda mutum zai kare kansa daga fada wa tarkon wadannan masu kutsen.

Advertisement

Bullar Cutar Gansakuka Ta Sa Manoman Citta Tafka Mummunar Asara A Kaduna

Sabuwar hanyar da a yanzu suke amfani da ita shi ne yaudara. Da zarar sun yi nasarar kwace Facebook account na wani, to sai su bi abokansa na Facebook din ta messenger, sai su yi ta tura sako, suna cewa a ka tura musu lambar wayarka, za su baka kyautar data na browsing mai yawan gaske.
Wasu 250 GB wasu kuma 500 GB. To da zarar ka ga haka, to wannan mai Facebook account din hackers sun kwace masa Facebook. Idan kuwa ka tura musu, za su ce an turo maka wani code, ka turo mana shi. Kana tura musu, shikenan baka da iko da Facebook account dinka, sun kwace maka shi.
Kar ka yadda wani yace ka tura masa lambar wayarka ko email, ka tura masa.

Mafi yawan mutane idan sun bude shafin Facebook ba sa la’akari da seta wasu abubuwan, musamman wadanda suka shafi layin tsaro kamar boye wasu muhimman sirruka game da mutum kansa.
wasu daga cikin mutane idan sun bude shafin Facebook, sukan yi amfani da makullan sirri mafi sauki ta yadda ba za su taba mantawa ba, mafi rinjaye daga cikin su, suna amfani da lambobin wayarsu lambar kuma wanda suka riga suka yi rijista wajen bude shafin Facebook din da shi.

Shin laifi ne amfani da lambar waya a matsayin makullin sirri ‘password’? A’a ba laifi ba ne amma akwai bukatar boye lambar wayar daga masu bude ko bincika shafin ‘profile’ din mutane don ganin sirrukansu ko samun lambobin su.

Advertisement

Yana da matukar muhimmanci mu san cewa masu kutse cikin shafin mutane na Facebook, mafi yawa daga cikin su ta hanya mafi sauki suke iya shiga, shi ne rashin tsaro da kuma rashin ba da muhimmancin da muke yi wa shafin na Facebook. Daga mun fara amfani da shafin muna ‘chatting’ shikenan bamu damu da kulawa ba.

Abubuwan da ya kamata mu kiyaye sun hada da boye sirrukan mu masu muhimmanci irin su lambar waya, Email, shekarun haihuwa (Date of Birth) da sauransu, kuma muke yawan kara saka masa tsaro musamman akwai abubuwan da ake kira code generator, two factors authentication da sauransu.

Ya kamata kuma kasan ‘where you’re logged in’ ko da za ka sayar da wayar ka to ka tabbatar ka sauke shafinka na Facebook daga cikin wayar. Wato za ka yi ‘log out’ kenan. Sannan yana da kyau idan za ka canza waya ka goge dukkan abin da ke kan wayar ta hanyar shiga setting na kan wayar, sai ka shiga ‘factory data reset’.

Advertisement

Mutane da dama suna yawan kuka da yadda ake kwace musu shafinsu na Facebook, alhali shafin yana da muhimmanci a wurin su, wasu na da abokai makusanta da wadanda ke nesa, kamar kasashen waje, kuma ta wannan sahar Facebook din ce kadai suke haduwa, wasu kuwa sun shahara da shafinsu na Facebook din, ma’ana suna da mabiya da yawa wanda lalacewar shafin kan iya haifar musu da matsala ta rashin dawo da wasu cikin mabiyan nasu, ko wani al’amari na siyasa ko kasuwanci da suke tallata wa ta shafin nasu na Facebook.

Sau da yawan lokuta mutane sukan bude shafin Facebook haka kawai ba tare da bin matakai na Facebook din ba, daga sun bude shafin Facebook din, sukan fara amfani da shi ne kai tsaye ba tare da tunanin seta wasu abubuwa da zai saukaka musu amfani da Facebook din ba, ko kuma kakaba wa shafin tsaro mai yawa domin kiyaye lafiyar shafin Facebook din daga baragurbin mafarauta (Hackers).

Daga lokacin da mutum ya bar shafinsa na Facebook haka kawai ba tare da tsaro ba, ta hanya mai sauki za a iya kutsawa a bata masa shafin na sa, ko a maka kwacen shafin Facebook gabadaya, sai dai ka ga ana saka abubuwa a shafin na ka kai kuma baka sani ba, ko kuma ka ga an tura sakon rokon kudi a wajen jama’a har da wadanda kake jin kunya da ganin girmansu.

Advertisement

Lokacin da aka kwace wa mutum shafinsa na Facebook, abu na farko da suke yi shi ne canza wa mutum makullin sirri ‘password’ sannan su shiga su canza duk wata hanya ko kafar da za a iya bi don dawo da shafin, bayan nan sai su goge duk wani rubutu ko hoto da ke cikin shafin Facebook din (amma idan sun ga dama, domin ba kowane a cikinsu ke yin hakan ba), canza wa mutum hoton dake a kan ‘Profile’ dinsa shi ne abu na karshe da suke bayan sun canza wa mutum suna.

Idan har sun goge lambar wayarka da email, to hakan yakan ba da wahala sosai wajen dawo da shafin Facebook din, domin kuwa sun toshe saukakan hanyoyin da za a bi don a kwato Facebook account din. Ko da an yi nasarar kwato shafin na ka, to wasu abubuwan ma basa dawowa, sai dai daga karshe ka ji mutum yana cewa ba ya jin dadin shafin na sa na Facebook din.

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *