Connect with us

News

An Hallaka ’Yan Bindiga 4, An Kama Wasu 13 A Jahar Kaduna

Published

on

Dan sanda akan aiki

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna, ta Hallaka wasu mutane hudu da ake zargi da garkuwa da mutane tare da cafke wasu 13 a wani samame da ta kai a sassan jihar ta kaduna.

Advertisement

Da yake bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargin, mukaddashin kakakin rundunar, ASP Manir Hassan, ya shaida wa manema labarai cewa, an hallaka wadanda ake zargin ne a yayin da aka yi artabu a sassa daban-daban a Jihar Kaduna.

Shugaban Gwamnatin Kasar  Jamus Zai Ziyarci Najeriya

A cewar kakakin ‘yan sandan, daga cikin wadanda ake zargin akwai Auwal Saidu, wani jami’in tsaro mai zaman kansa, wanda ake zargin shi ne ya kitsa sace uban gidansa, sannan ya karbi naira miliyan 10 a matsayin kudin fansa kafin shi da ‘yan kungiyarsa su sako wanda lamarin ya rutsa da shi.

Wasu daga cikin kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da bindigogi kirar AK-47 guda biyu da babura biyu da kunshin harsashi 15 da kuma buhun tabar wiwi.

Advertisement

Kakakin ‘yan sandan ya bayyana cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Wani labarin kuma Shugaban Gwamnatin Kasar  Jamus Zai Ziyarci Najeriya

 

Advertisement

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

Advertisement

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *