Connect with us

News

Darajar Naira ta ragu a kasuwar masu zuba jari da fitar da kayayyaki

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Darajar Naira a jiya Litinin ta rabu da Dala a yayin da ake musayar ta a kan Naira dari 773.50 a fannin masu zuba jari da masu fitar da kayayyaki.

Advertisement

Farashin Naira ya ragu da kashi 7.08 bisa dari a kan N736.62 da aka yi wa dala a ranar 8 ga watan Satumba.

Kungiyar Likitoci Ta Nesanta Kanta Da Wani Likita Da Ake Zargi Da Sace Kodar Mutum

Farashin ya rufe kan N771.49 zuwa Dala a jiya Litinin din.

Har sai da Dala ta kai N804.15 inda shine mafi girman farashin da aka samu a cinikin na jiya kafin ya daidaita akan N773.50.

Advertisement

Ana siyar da Naira a kan N722.39 ga Dala a kasuwar ranar.

An yi cinikin dala miliyan 37.86 a kasuwar masu zuba jari da masu fitar da kayayyaki a jiya Litinin.

Wani labarin kuma Kungiyar Likitoci Ta Nesanta Kanta Da Wani Likita Da Ake Zargi Da Sace Kodar Mutum

Advertisement

 

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

 

Advertisement

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

 

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

Advertisement

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *