Connect with us

News

Kungiyar Likitoci Ta Nesanta Kanta Da Wani Likita Da Ake Zargi Da Sace Kodar Mutum

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Kungiyar likitocin ta nageriya NMA reshen jihar Plato ta nesanta kanta daga alaka da Dr Noah Kekere, wanda aka kama bisa zargin satar kodar wata mata.

Advertisement

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa  ‘yan sanda sun kama wanda ake zargin ne a garin Jos bayan wani dan kasuwa, Alhaji Kamal, ya zarge shi da cire kodar matarsa a lokacin da aka yi ma ta tiyata a shekarar 2018.

ZARGIN MAITA: Mahaukaciya Ta Razana Al’umma A Jahar Kaduna

Da yake mayar da martani, shugaban kungiyar NMA a jihar, Dr Bapigaan William Audu, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce a binciken da suka yi kan al’amarin, ya nuna cewa Kekere ba likita ba ne.

A cewar sanarwar, binciken kwakwaf da kungiyar ta yi, ya nuna cewa shi mutum ne mai kwarjini da ke sojan gonad a nuna cewa shi likita ne.

Advertisement

A wani labarin kuma ZARGIN MAITA: Mahaukaciya Ta Razana Al’umma A Jahar Kaduna

 

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

Advertisement

 

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

 

Advertisement

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

 

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

Advertisement
Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *