Connect with us

News

Mataimakin Gwamnan Jihar Edo Ya Fara Kwashe Kayan Offishinsa Daga Gidan Gwamnati

Published

on

Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki da kuma Mataimakin gwamnan jihar Edo Philip Shuaibu

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shuaibu ya fara mayar da ofishinsa zuwa wani wuri da ke kusa da gidan gwamnatin jahar.

Hakan dai ya biyo bayan janye karar da Shuaibu ya shigar a gaban babbar kotun tarayya a makon da ya gabata domin dakatar da zargin gwamnan jihar Godwin Obaseki na tsige shi daga mukaminsa na Mataimakin gwamnan jihar Edo

Darajar Naira ta ragu a kasuwar masu zuba jari da fitar da kayayyaki

Sabon ofishin yana lamba 7, Dennis Osadebey Avenue, kusa da gidan gwamnatin jihar ta Edo.

Majiyoyi sun shaidawa manema labarai cewa shugaban ma’aikata ya aike da wasika zuwa ga babbar sakatariya a ofishin mataimakin gwamnan inda ya umarce ta da ta kula da zirga-zirgar ma’aikatan gwamnati da fayil-fayil zuwa sabon ofishin.

An kuma rawaito cewa sabon ofishin babu wutar lantarki kuma wurin kwanciyar ruwa ne sannan ofisoshin sunyi kankanta.

Sai dai gwamnatin jihar ta dage cewa sabon ofishin mataimakin gwamnan yana cikin yankin da aka ware a matsayin gidan gwamnati.

Wani labarin kuma Darajar Naira ta ragu a kasuwar masu zuba jari da fitar da kayayyaki

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement