Connect with us

Politics

Jam’iyyar NNPP Na Neman Kawo Karshen Yarjejeniyar Da Kwankwasiyya

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Jam’iyyar New Nigerian People Party NNPP ta rubutawa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC wasika akan shirin da wasu mutane ke yi na sauya tambarin jam’iyyar.

Haka kuma Jam’iyyar ta kuma rubutawa Sanata Rabi’u Kwankwaso, dan takararta na zaben shugaban kasa wasika, domin ya kawo karshen yarjejeniyar fahimtar juna da ta shiga da kungiyar Kwankwasiyya.

Jam’iyyar APC  Na Shirin Fara Sabuwar Rijista Ga Mambobinta Gabanin Shekarar 2027

Duk wasikun biyu dai sun samu sahannun lauyan jam’iyyar, Mista Peter Ogah, a ranar laraba.

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Idan za a iya tunawa dai a ranar 5 ga watan Satumba ne wani bangare na jam’iyyar ya kori Kwankwaso bisa zarginsa da zagon kasa, amma a ranar aka samu umarnin kotu wanda ya hana dakatarwar da aka yi masa.

Wani labarin kuma Jam’iyyar APC  Na Shirin Fara Sabuwar Rijista Ga Mambobinta Gabanin Shekarar 2027

 

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement