Connect with us

News

Wata Ta Kardama Ta Kunno Ka Tsakanin Gwamnati Da Makarantu Masu Zaman Kansu A Jihar Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Wani rikici ya kunno kai a fannin ilimi a Kano yayin da gamayyar kungiyoyin masu makarantu masu zaman kansu ke barazanar daukar matakin shari’a akan Comrade Baba Abubakar Umar, mai baiwa gwamna shawara na musamman kan zargin abun suka bayyana amatsayin ikirarin karya da wasu kalamai na cin zarafi da tsarotarwa da yake yi akansu.

Ƙungiyoyin sun bukaci mai bada shawara na musamman ga gwamnan kan makarantu masu zaman kansu da ya fito fiti ya nemi Afuwarsu a bainar jama’a ba tare da wani sharadi ba, wanda rashin yin hakan ka iya tunzura kungiyar ga daukar matakin shari’a

Jam’iyyar NNPP Na Neman Kawo Karshen Yarjejeniyar Da Kwankwasiyya

Da yake jawabi a madadin gamayyar da yammacin ranar  Laraba, daya daga cikin masu ruwa da tsaki na kungiyoyin, Injiniya Bashir Adamu Aliyu, ya ce Baba Umar ya zargesu da laifin yin jabun takardar rajista, rashin fitar da haraji ga gwamnati da karin kudin makaranta ba bisa ka’ida bad a raina gwamnati da dokokinta da kuma Tsauwalawa Iyayen yara da dai sauransu.

Aliyu, yayin da yake musanta dukkannin ikirarin, ya bukaci Gwamna Abba Kabir ya sanya baki domin masu Makarantu masu zaman kansu na cikin masu ruwa da tsaki a jihar Kano dake tallafawa Ilimi.

Da yake mayar da martani, Baba Abubakar Umar ya bukaci kungiyoyin da su aiwatar da barazanarsu, inda ya jaddada cewa dole ne masu makarantun su bi dokar makarantu masu zaman kansu ta 2014.

Wani labarin kuma Jam’iyyar NNPP Na Neman Kawo Karshen Yarjejeniyar Da Kwankwasiyya

 

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

 

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

 

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

 

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement