Connect with us

News

2023: Kwamishinan Yan Sanda Ya Gayyaci Shugabannin APC Da NNPP, Gabanin Hukuncin Kotu Kan Zaben Gwamna A Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mohammed Usaini Gumel, a ranar Alhamis, ya gayyaci shugabannin jam’iyyar NNPP da na APC, a wani taron zaman lafiya da aka shirya domin kawo karshen duk wata fargabar tashin hankali, gabanin yanke hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamna a jihar Kano zata yi.

Duubban magoya bayan jam’iyyar NNPP ne dai suka gudanar da addu’o’i na musamman a fadin kananan hukumomin jihar 44, a ranar Alhamis, inda suka nemi taimakon Allah domin samun nasara a kotun.

Yan Kwankwasiyya Sun Gudanar Da Sallar Samun Nasara A Kotun Zabe.

Da yake daukar matakan dakile duk wata barazana ko fargabar tashe-tashen hankula da ke kunno kai a tsakanin mazauna Kano, Kwamishinan ‘yan sanda Gumel ya gayyaci shugabannin jam’iyyun siyasar biyu a jihar nan domin taron sulhu.

Advertisement

Wata sanarwa da CP Gumel da kansa ya sanya wa hannu kan muhimman batutuwan ta nuna cewa shugabannin jam’iyyun siyasar biyu sun rungumi zaman lafiya tare da ba da tabbacin cewa za su amince da sakamakon da kotun ta yanke da zuciya daya.

Wani labarin kuma Yan Kwankwasiyya Sun Gudanar Da Sallar Samun Nasara A Kotun Zabe.

 

Advertisement

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

Advertisement

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *