Connect with us

News

Jami’ar Chicago ta fitar da sanarwa kan bayanan karatun Tinubu

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Jami’ar jihar Chicago CSU ta tabbatar da cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya halarci jami’ar Kuma ya kammala karatun digiri a shekarar 1979.

Makarantar ta kuma tabbatar da cewa tsohon gwamnan na Legas ya kammala karatun digiri a shekarar 1979.

Har Yanzu Babu Takamaimiyar Ranar Dawo Da Ayyukan Jiragen Daular Larabawa A Najeriya

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’ar ta fitar ga kafar sadarwa ta CBS News.
“A matsayin cibiyar ilimi, a wasu lokuta ana tambayar mu don samar da bayanan da suka shafi bayanan dalibai,” in ji makarantar a cikin wata sanarwa da aka bayar ga CBS.

Makarantar, duk da haka, ta bayyana cewa akwai dokar tarayya, wacce aka sani da Dokar Haƙƙin Ilimin Iyali da Sirri, FERPA, wanda ke kare sirrin bayanan ɗalibai da iyakance abin da wata cibiya za ta iya bayyanawa.

Ta ci gaba da bayanin cewa “A watan Agustan 2023, an gabatar da bukatar kotun tarayya ta Amurka cewa jami’ar ta ba da bayanai da suka shafi bayanan ilimi da suka shafi Bola Tinubu, Shugaban Najeriya, kuma tsohon dalibin jami’ar CSU.

“Jami’ar ta tabbatar da cewa Tinubu ya halarci CSU kuma ya kammala karatunsa a 1979 da digirin farko. Dokar tarayya, duk da haka, ta hana mu samar da wani ƙarin bayani ba tare da izini ba ko sai dai idan an ba mu izinin yin hakan ta hanyar umarnin kotu.

Wani labarin kuma Har Yanzu Babu Takamaimiyar Ranar Dawo Da Ayyukan Jiragen Daular Larabawa A Najeriya

 

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

 

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement