Connect with us

News

Rundunar Yan Sandan Jahar Gombe Tace Mutum 67 Ne Suka Bace Cikin Watanni Tara

Published

on

DAGA  KABIRU BASIRU FULATAN

A kalla mutane 67 ne rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta sanar da batan su tsakanin watan Janairu zuwa Satumbar 2023.

Da yake tabbatar da hakan a wata tattaunawa ta musamman da wakilinmu, jami’in hulda da jama’a na jihar, ASP Mahid Abubakar, a ranar Asabar, ya ce an samu shari’oin a fadin kananan hukumomin jihar 11.

Advertisement

Dan Sahu ya Maida Miliyoyin Ku’di daya Tsinta

Bisa binciken da wakilinmu ya gudanar a watan Agusta mutane kusan 65 ne aka bayyana bacewarsu, inda binciken da aka gudanar ya kawo adadin zuwa 67 a watan Satumba.

A cewar Abubakar, kararrakin sun fara ne daga watan Janairun 2023 zuwa Satumba, inda ya kara da cewa ana kokarin ganin an dawo da wadanda lamarin ya shafa.

“Daga watan Janairu zuwa yau muna da kararraki 67 na bacewar mutane a hedikwatar,” in ji shi.

Advertisement

Abubakar ya bayyana cewa duk da cewa ’yan uwansu sun gano wasu daga cikin wadanda suka bace, yana mai jaddada cewa rundunar da ke karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sanda Oqua Etim, ta himmatu wajen tabbatar da tsaron mazauna yankin.

“Bari in kara da cewa an samu wasu daga cikin mutanen da suka bata. ‘Yan uwansu ne suka bayar da rahoton kararrakin, kuma wasu daga cikin wadanda suka bace sun koma gida.

“Ina kara tabbatar muku da sauran jama’ar jihar cewa Gombe tana cikin koshin lafiya a matsayinsa na kwamishinan ‘yan sanda Oqua Etim tare da mutanensa sun himmatu wajen tabbatar da tsaron jihar da al’ummarta, babu bukatar damuwa,” Abubakar ya kara da cewa.

Advertisement

Wani labarin kuma Dan Sahu ya Maida Miliyoyin Ku’di daya Tsinta

 

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

Advertisement

 

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

Advertisement

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

 

Advertisement
Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *