Connect with us

News

Kotu ta Sanya Ranar Yanke Hukuncin Zaɓen Gwamnan Jahar Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Kotun sauraron kararrakin zabe ta sanya ranar Laraba 20 ga watan Satumba domin yanke hukuncin Shari’ar kujerar Gwamnan Kano.

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Idan za’a iya tunawa bayan kammala zaɓen gwamnan jihar kano wanda hukumar zabe ta bayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben, hakan tasa jam’iyyar APC ta shigar da Kara gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar domin ƙalubalantar zaben.

An Daure Mai Unguwa A Kan Zargin Satar Ƙofofi A Kano

A cikin wata sanarwa da ta fito daga Kotu sauraren kararrakin zaben Mai dauke da sa hannun maga takardar kotu , tace za’a gudanar da zaman yanke hukuncin ne a babbar Kotun jihar kano dake Miller Road a Kano.

Hukuncin kotun dai shi zai tabbatar da halastaccen wanda ya ci zaɓen, duk kuwa da cewa akwai damar daukaka kara ga duk wanda bai aminta da hukuncin kotun sauraren kararrakin Zaben gwamnan ba .

Yanzu haka dai al’ummar jihar Zamfara suna dakon zuwan ranar litinin din domin hukuncin da kotun zata zartar.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement