Connect with us

News

Wani bawan Allah ya Gwnagwaje Auwalu Salihu da Sabon Adaidaita Sahu.

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Wani bawan Allah ya Gwnagwaje Auwalu Salihu da Sabon Adaqqidaita Sahu.

In Baku manta ba shine wanda ya tsinci Naira Miliyan 15 kuma ya mayar wa maishi bayan yaji sanarwa a Arewa Radio 93.1.

Jam’iyyar APC ta lashi takobin kama duk wani dan Najeriya mazauna amurka da ya yi zanga-zangar adawa akan Tinubu

Sakamakon wannan abin kirki da yayi, Alhaji Bashir Gentile ya kai yaron gidan wani Babban Mai Arziki anan Kano, inda ya bashi wannan sabon adaidata sahu don Wanda Yaron yake amfani da shi na haya ne. Kuma yayi ummarni a maidashi ya koma makaranta, ya dauki nauyin karatunsa har Sai ya gama.

Wani labarin kuma Jam’iyyar APC ta lashi takobin kama duk wani dan Najeriya mazauna amurka da ya yi zanga-zangar adawa akan Tinubu

 

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

 

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

 

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

 

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement