Connect with us

News

Dillalan Man Fetur Na Barazanar Dakatar Da Ayyukana Su Saboda ƙarin kuɗaɗen haraji

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

‘Yan kasuwa masu sayar da man fetur sun bayyana yiwuwar dakatar da ayyukansu, saboda ƙarin kuɗaɗen haraji da suka yi zargin gwamnati na yi.

Sun kuma bayyana ci gaba da biyan hukumar kula da harkokin sufurin jiragen ruwa ta NIMASA da dalar Amurka maimakon naira, da ƙara dagula al’amura.

Tarihin Alƙaliyar da zata yanke hukuncin shari’ar zaɓen gwamnan Kano

Tashin farashin man fetur da na kayan abinci da sufuri na daga cikin dalilan da hukumomi suka ce na janyo hauhawar farashi, lamarin da ke jefa miliyoyin ‘yan ƙasar nan cikin ƙangin rayuwa da matsin tattalin arziƙi.

 

Wani jami’i a cikin dillalan man fetur ɗin, Bashir Ahmed DanMallam ya ce zasu dakatar da ayyukan man fetur dinne gaba-daya saboda wasu dalilai.

Dan Malam yace na farko gwamnati ya kara haraji akan man Dizal, wanda kuma man da ake zubawa a manyan motocin da ake dauko fetur din da shi.

Na biyu akwai maganar harajin tashoshin jiragen ruwa da na hukumar NIMASA, wanda yace har yanzu da Dalar Amurka ake biyan waɗannan kudaden maimakon Naira, yace kuma kowa ya san yadda Dalar Amurka take a kasuwa, daga karshe ko a kara kudin man, ko a tsaya da saida shi.

Na uku shi ne rashin kyawun hanyoyin da ake dakon man musamman a arewacin Najeriya, babu hanyoyin dakon man masu kyau.

Na hudu akwai mutane da suka ciwo bashi da kuɗaɗen bankuna wanda suka sanya a hukumar daidaita farashin man wato (PEF) amma aka rike musu kudaden.

Ya ce dayawa sun karye, sun rufe gidajen man, basa iya gudanar da sana’ar saboda an rike musu kudaden na su.

Bashir Dan Malam ya ce shi kan shi kamfanin NNPC da yake bada kudin mota nan gaba sai ya daina saboda bazai iya ba.

A karshe doke sai an tsaya cak, gwamnatin ta shigo. Ya zama wajibi a dawo da biyan kudin NIMASA da Naira amma ba da Dalar Amurka ba a cewar jami’in.

 

Ya ce nan gaba kadan zasu fitar da sanarwar matakan da zasu dauka, watakila ma su dakatar da ayyukan su ma gaba daya a fadin kasar nan.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement