Connect with us

News

Yakin Da Ake Yi A Sudan Ya Fantsama Zuwa Yankin Port Sudan

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Yakin da ake yi tsakanin sojojin dake gaba da juna a sudan ya fantsama zuwa yankin port Sudan, karo na farko kenan da samun rikin a yankin tun faro yakin sama da watanni 5.

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Sojojin sudan sunyi musayar wuta da wasu sojojin hadin gwiwa na kasar.

Kotu ta soke nasarar da kakakin majalisar dokokin jihar Gombe ya samu.

Dakarun sunyi kokarin janye shinge daka sojojin yankin suka kafa a tsakiyar birnin.

Port sudan shine birnin da jami’an gwamnatin da hukumomin majalisar dinkin duniya suka kaura biyo bayan rikicin da ya dai-daita babban birinin kasar Khartoum. Rikici tsakanin sojin sudan da dakarun kai daukin gagagwa na RSF,yayi sanadiyyar mutuwar mutane da raba dubban mutane da muhallan su tun bayan fara yakin a watan Afrilu.

Wani labarin kuma Kotu ta soke nasarar da kakakin majalisar dokokin jihar Gombe ya samu.

 

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement