Connect with us

News

Kwanaki 100: Kotun Zabe Ta Tsige ‘Yan Majalisar Wakilai 25, Sanatoci 5 Na APC, PDP, LP da NNPP

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Sama da kwanaki 100 bayan rantsar da majalisar tarayya ta 10, aƙalla ‘yan majalisar wakilai 25 da Sanatoci 5 Kotu ta tsige daga kujerunsu Jam’iyyar APC ce ta fi kowace jam’iyya rasa Sanatoci yayin da kuma ita ce ta fi amfana da hukuncin kwace kujerun mambobin majalisar wakilai Zuwa yanzu, PDP ta rasa kujerun yan majalisar wakilai 12, Labour Party ta rasa 10 yayin da APC da NNPP suka rasa ɗaya kowace

Advertisement

Akalla mambobin majalisar wakilan tarayya 25 da Sanatoci 5 suka rasa kujerunsu kawo yanzu a Kotun sauraron ƙorafe-korafen zaɓe a faɗin Najeriya. Yayin da jam’iyyar APC ce kan gaba wajen rasa kujerun Sanatoci a hukuncin da Kotu ta yanke, a ɗaya bangaren kuma ita ta fi amfana da hukuncin kwace kujerun mambobin majalisar wakilai.

Muhimman Ayyuka 10 Da Abba Ya Yi A Kwana 100 A Kano–Hafsat Aminu Adhama

Waannan ta faru ne duk a cikin kwanaki 100 bayan magatakardan majalisar dattawa da na Majalisar Wakilan Tarayya sun rantsar da majalisa ta 10. A halin yanzu, mafi akasarin ‘yan Majalisun da suka yi rashin nasara a Kotu na jam’iyyun APC, PDP, Labour Party da NNPP mai kayan marmari sun lashi takobin ɗaukaka ƙara.

Sanatocin da APC da PDP suka rasa zuwa yau A mazaɓar Sanatan Kogi ta gabas da na Kogi ta tsakiya, Kotun zaɓe ta soke nasarar jam’iyyar APC mai mulki, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Advertisement

Haka nan kuma jam’iyyar APC ta sake rashin nasara a Kotu, inda aka rushe nasarar Sanatocinta a mazaɓar Delta ta tsakiya da kuma Delta ta kudu. Bayan haka Kotun zaɓe ta rushe nasarar jam’iyyar PDP a mazaɓar Sanatan jihar Filato ta kudu.

Jerin jihohin da za a gudanar cikon zaɓe Kotun zaɓe ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta shirya ƙarishen zabe a mazaɓar Delta ta tsakiya, Delta ta kudu da Kogi ta gabas cikin kwanaki 90 masu zuwa.

A ɗaya bangaren, Kotun ta tsige mambobin majalisar wakilan tarayya 26 zuwa yanzu, sai dai Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta maida ɗaya daga cikinsu. Jam’iyyar PDP ta rasa mambobin majalisar wakilai 12 yayin da Labour Party ta rasa guda 10. Jam’iyyar APC da kuma NNPP sun rasa ɗai-ɗai. Kotu Ta Tsige Dan Majalisar PDP, Ta Tabbatar da Nasarar ‘Yan Takarar APC 2 a Taraba

Advertisement

A wani rahoton kuma Kotun zabe mai zama a Jalingo ta kwace kujerar dan majalisar dokokin jihar Taraba na jam’iyyar PDP. Bugu da ƙari, Kotun ta tabbatar da nasarar wasu ‘yan takarar jam’iyyar APC a zaben mambobin majalisar jihar da ya gabata ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *