Connect with us

News

Barr Olisa Agbakoba yace hukuncin zaben Kano cike yake da kura-kurai

Published

on

Barr Olisa Agbakoba

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Tsohon Shugaban Kungiyar Lauyoyin Nigeria Barrister Olisa Agbakoba (SAN) ya jaddada cewa Hukuncin da Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Jihar Kano ta yanke kan zaben Gwamnan Jihar Kano cike yake da kurakurai.

Cutar Mashako Ta Yi Sanadin Mutuwar Yara 14 A Jihar Jigawa

Jaridar Indarank ta rawaito Olisa Agbakoba yace ya rasa inda Alkalan Kotun Sauraren Kararrakin Zaben data saurari Shari’ar Gwamnan Jihar Kano ta samo hurumin soke wasu Kuri’u na wata Jam iya a matsayin ta na wacce ba hukumar zaɓe mai zaman kanta ba.

Agbakoba ya ƙara da cewa sannan ya rasa inda Kotun Sauraren Kararrakin zaɓen gwamnan jihar Kano ta samo hurumin iya aiwatar da wani hukunci kan wata Shari’a ta hanyar Manhajar zoom ba tare da Alkalan sun halarci zama a cikin Kotun Sauraren Kararrakin Zaben ba.

Ya kara da cewa, babu wata doka a duk Duniya da ta yadda wasu Alkalai su buya a wani waje su yanke hukunci kan wata Shari’a ana haskawa wakilan masu Kara da wadanda ake Kara ta hanyar haskasu a Majigi, saboda wata Barazanar rashin tsaro ba.

Olisa yace dokar cewa tayi duk runtsi se Alkalan sun halarci zaman Kotun ta hanyar tsaurara tsaro, amma babu wani Dalili da zai sa su buya a wani waje suyi hukunci ba tare da suna gaban masu Kara da wadanda ake ƙara da wakilan su ba.

Yace wannan ya sabawa sashi na 19 na kundin tsarin mulkin Nigeria gaba daya ne, wanda yayi magana kan kula da hakkin ɗan kasa a dokance.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement