Connect with us

News

Yan Bindiga Sun Kai Wani Sabon Hari A Kaduna Sun Kashe Mutum 6

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Wasu ‘yan bindiga a daren ranar Talata sun kutsa kai yankin Takanai a masarautar Atyap da ke karamar hukumar Zango Kataf ta jihar Kaduna, inda suka kashe mutum shida daga cikin wadanda lamarin ya ritsa da su akwai yara kanana guda biyu.

An kai sabon harin kwanaki biyar bayan wani hari da aka kai a Kaura inda aka kashe wata mata tare da yin garkuwa da ‘ya’yanta biyu.

Naira Marley Yace Bashi Da Hannu A kashe Mohbad kuma Ni Ba Dan Kwaya ko Kungiyar Asiri

Mukaddashin sakataren yankin, Samson Markus, wanda ya tabbatar da faruwar harin a ranar Larabar nan, ya ce ‘yan bindigar sun kai hari kauyen da misalin karfe 7 na dare, inda suka bude wuta suka kashe mutane hudu a wuri guda, sai kuma karin wasu biyun daban.

“Muna cikin gudanar da harkokinmu na yau da kullum sai muka ji karar harbe-harbe, sai muka dauka sojoji ne tun da farko sai muka ga ‘yan bindiga ne, sun shigo ne daga garin Zango don kai hari.” cewar ganau

Ya ci gaba da cewa, “Kafin sojoji su iso sun yi nasarar kashe mutum shida ciki har da yara 2, zuwan sojojin ne ya ba su tsoro suka tafi da su suka bar yankin.

 

“Abin takaici ne irin wannan abin bakin ciki da ke ci gaba da faruwa a Kauyukanmu da muka yi tunanin al’amura sun dawo sun fara saisaita. Muna yi kira ga gwamnati da sojoji da su rubanya kokarinsu tare da yaki da wadannan ‘yan ta’addar da suka mamaye kauyuka suna kashe mutanen da ba su ji ba -ba su gani ba.”

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ba ta mayar da martani kan harin ba, domin har zuwa lokacin da muke wannan rahoton kuma ta kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, bamu iya nasarar samunsa ba.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement