Connect with us

Sport

Bamu Da Niyyar Cin Zarafin Dan Wasa Victor Osimhen-  Napoli 

Published

on

Victor Osimhen

DAGA MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Kungiyar Napoli ta mayar da martani ga wani faifan bidiyo na TikTok mai cike da cece-kuce akan dan wasanta kuma dan Najeriya, Victor Osimhen.

A wannan makon, an ba da rahoton cewa Osimhen na iya daukar matakin shari’a a kan Napoli saboda wani faifan bidiyo na TikTok wanda yake shagube akan Osimhen saboda ya barar da bugun fanareti yayin karawa da Bologna a wasan Seria A.

 

Lauyoyin Atiku Sun Shigar Da Kara Suna Kalubalantar Zuwan Tinubu Jami’ar Chikago

Amma, kungiyar ta Serie A a cikin wata sanarwa ta ce ba za ta iya yi wa Osimhen shagube ba, wanda ta ke daraja shi a matsayin dan wasa.

Idan Victor na ganin wannan shagubene akansa to wannan ba shine abin da kulob din ya nufa ba.

Idan zaku tuna Leadership Hausa ta bayyana cewar a ranar Talata da yamma, wakilin Osimhen Calendar ya bayyana cewar zasu dauki matakin shari’a akan Napoli kungiyar.

Wani labarin kuma Lauyoyin Atiku Sun Shigar Da Kara Suna Kalubalantar Zuwan Tinubu Jami’ar Chikago

 

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

 

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

 

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

 

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

 

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement