Connect with us

Entertainment

An Lakadawa Jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya Duka A Jahar Kano

Published

on

fitacciyar matashiya ‘yar Tiktok din nan Murja Ibrahim Kunya

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Wasu da ba a san ko suwaye ba sun yi wa fitacciyar matashiya ‘yar Tiktok din nan Murja Ibrahim Kunya dukan tsiya a yammacin ranar Alhamis a Kano.

Advertisement

A hotunan matashiyar da suka bayyana a shafukan sada zumunta da har Jaridar Inda Ranka ta samu gani bata-garin sun canza mata kama da raunuka a fuskarta.

Bamu Da Niyyar Cin Zarafin Dan Wasa Victor Osimhen-  Napoli 

Tuni dai aka fara yin kira ga jami’an tsaro da su bi mata hakkinta ta hanyar zakulo wadanda suka yi mata wannan aika-aika.

Murja Ibrahim Kunya dai tayi kaurin suna a shafin TikTok inda take da mabiya masu dimbin yawa,dake bibiyar shafin nata.

Advertisement

Kuma yar gwagwarmayar siyasa ce da take goyon bayan Gwamnan jahar Kano Eng Abba Kabir Yusuf.

Wani labarin kuma Bamu Da Niyyar Cin Zarafin Dan Wasa Victor Osimhen-  Napoli 

 

Advertisement

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

 

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

Advertisement

 

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

 

Advertisement

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *