Connect with us

News

Rundunar ‘Yan sanda sun kama mutum 6 kan kisan wani dalibin jami’ar tarayya ta Katsina

Published

on

Dan sanda akan aiki

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN. 

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wasu dalibai shida na jami’ar tarayya ta Dutsinma bisa zargin kashe wani matashi mai suna Abubakar Nasir-Barda dan shekara 21 da haihuwa dan level  200.

Advertisement

ASP Aliyu Abubakar-Sadiq, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Katsina ranar Asabar.

Nigeria@63:Hare-Haren ‘Yan Bindiga A Jihar Filato Ya Sa Daruruwan Mutane Sun Rasa Matsugunansu

Abubakar-Sadiq ya yi watsi da rade-radin da ake yi na cewa an kashe marigayin ne saboda al’amuran addini.

“A ranar 28 ga Satumba, 2023, wani mummunan lamari ya faru a unguwar Darawa da ke karamar hukumar Dutsinma, wanda ya shafi dalibai takwas na Jami’ar Tarayya ta Dutsinma.

Advertisement

 

“Lamarin ya faru ne sakamakon zazzafar cece-ku-ce tsakanin daliban kan alakarsu da wata daliba mace, lamarin da ya yi kamari, wanda ya kai ga mutuwar daya daga cikin daliban da lamarin ya shafa.

A cewarsa, rundunar ta dauki lamarin da muhimmanci kuma a halin yanzu tana gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar lamarin.

Advertisement

Ya ce rundunar ta na aiki tukuru don tattarawa da kuma tantance duk wasu shaidun da ake da su dangane da lamarin.

 

Kakakin rundunar ya ce yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, za a raba bayanai ga jama’a domin tabbatar da gaskiya.

Advertisement

Abubakar-Sadiq ya kuma ce rundunar za ta yi maraba da duk wanda ya samu labarin akan  faruwar lamarin na gaskiya.

Ya ba da tabbacin cewa duk bayanan da aka samu za a bi da su da cikakken sirri.

“Kwamishanan ‘yan sandan jihar, Aliyu Abubakar-Musa ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu.

Advertisement

“Ya kuma mika ta’aziyyarsa ga ‘yan uwa da abokan arziki da wannan bala’i ya shafa da kuma mahukuntan Jami’ar.

A halin da ake ciki, Malam Nasir Ibrahim-Barda, mahaifin marigayin, ya bukaci ‘yan sanda su yi bincike sosai kan lamarin.

Mahaifin marigayin, a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN, ya ce duk wanda aka samu da laifi a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada domin gudun faruwar irin wannan lamari.

Advertisement

 

 

 

Advertisement
Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *