Connect with us

News

Gwamnatin Jihar Kano Zata Fara Bai Wa ‘Yan Mata 45,000 Tallafin N20, 000

Published

on

Gwamnan jahar Kano Abba Kabir Yusuf

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa, ta fara bayar da tallafin naira dubu ashirin-ashirin N20,000 ga ‘yan mata 45,000 domin tallafa wa harkokin karatunsu tare da karfafan iyayensu domin ci gaba da tura su zuwa makarantu a jahar Kano.

Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan acikin jawabinsa na ranar samun ‘yancin kan Nijeriya karo na 63 da ya gudana a dandamalin wasanni na Sani Abacha da ke birnin jahar  Kano.

Kungiyoyin kwadago suna duba yiwuwar janye batun tafiya yajin aiki bayan ganawa da gwamnatin tarayya 

Ya ce, “Domin agaza wa karatun yara mata da kuma karfafa wa iyayensu guiwa suke turasu zuwa makaranta, mun samar da wani tsarin tallafin naira N20,000 ga sama da ‘yan mata 45,000 a matsayin wani tsarin da zai ke taimaka wa harkokin karatunsu domin su cigaba da zuwa makaranta.

“Sannan, mun sake gabatar da tsarin motocin jigilar yara zuwa makaranta domin taimaka wa sufurinsu zuwa makaranta.”

Gwamnan ya kuma ce, gwamnatinsa ta na gina sabbin makarantu a fadin kananan hukumomi 44 da ke jihar a wani babban yunkuri da gwamnati ke yi na magance matsalar yaran da basu zuwa makaranta da suke gararanba a kan titina.

Kazalika, ya nanata aniyar tura daliban da suka kammala karatu da daraja ta daya (Fitst class) su 1,001 domin yin digirinsu na biyu a jami’o’in kasashen waje.

Sannan, ya ce, gwamnatinsa tana da muhimman tsare-tsare da shirye-shiryen da suka sanya a gaba da za su aiwatar a bangaren bunkasa harkokin koyo da koyarwa a jihar.

Wani Labarin kuma Kungiyoyin kwadago suna duba yiwuwar janye batun tafiya yajin aiki bayan ganawa da gwamnatin tarayya 

 

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

 

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

 

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

 

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement