Connect with us

News

Kalubale ga manya arewa: malamai da yan siyasa da sarakuna -Audu bulama bukarti

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

A cikin shirin fashin baki na su Barrister Audu Bulama Bukarti da kuma sauran abokansa Ja’afar Ja’afar edita na jaridar Daily Nigerian da kuma barrister Abba hikima da dan jaridar Freedom Radio nasiru zango.

Advertisement

Barrister Audu Bulama Bukarti yayi magana ne akan sace yan matan jami’ar tarayya ta Gusau a jihar Zamfara

Gwamnan Jahar Nasarawa Ya Lashi Takobin Ɗaukaka Kara Kan Soke Zabensa

Idan gwamnatin tarayya batayi wani abu ba, shin munga gwamnan jihar Zamfara ya tafi gurin shugaban kasa tunda yaran nan a garin Gusau anka dauke su.

Ko gwamna zamfara bashi da hakki ne zuwa inda shugaban kasa idan kace adawa ce lokacin da anka kai hari a Maiduguri zaka Kashim yaje inda shugaban kasa yana kuka da hawaye akan abinda yake faruwa a Maiduguri shi gwamnan Zamfara me yake yi.

Advertisement

Barrister majalisar Yan majalisu bata ce komai shi dan majalisar mai wakilta wajen yace wani abu, basu da sanata ne yace wani abu me sukeyi miye amfaninsu ?.

Kai saraunan gargajiya sun kasa tashi suyi abinda ya dace , malaman addini sun kasa tashi abinda ya dace suyi , yan siyasa sun kasa tashi suyi abinda ya dace suyi to yaya za’a yi kenan.

Ya kamata kowace kungiya addini su tsaya suyi magana akan a dawo da tsaro a yankin arewa idan sunkayi dan Allah suka dogara ga Allah to gwamnatin tarayya zata saurare su kuma za’a abinda yadace ayi.

Advertisement

Yan majalisa da sarakuna basuda amfani idan basu tashi sunkayi wani abu ba domin a samu ba gyara ba.wannan maganar tana daga cikin rashin tsaron da anka samu a cikin wannan mako da muke ciki yanzu yawan mutanen da a hannun yan bindiga Allah dai yasan yawan su.

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *