Connect with us

Entertainment

Me ya sa Tiwa Savage ta nemi ‘yan sanda su shiga tsakaninta da Davido

Published

on

Yansandan Najeriya sun fara gudanar da bincike kan shahararren mawaƙin nan na ƙasar Davido bayan ƙarar da abokiyar sana’arsa Tiwa Savage ta shigar a kansa, bisa zargin cin zarafinta da kuma yi mata barazana da rayuwarta.

Wani Matashi A Gombe Ya Kirkiri Injin Ban Ruwa Mara Amfani Da Fetur Ko Hasken Rana

A watan jiya ne tankiya ta ƙara ƙamari tsakanin mawaƙan biyu, bayan Tiwa ta sanya wani hotonta da na mahaifiyar ɗaya daga cikin ‘ya’yan Davido a shafinta na Instagram.

A ƙorafin da ta shigar a wajen ‘yansandan kamar yadda kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka ambato, Tiwa ta ce hoton da ta wallafa ya ɓata wa Davido rai, inda ya yi zargin ta yi hakan ne domin ta fusata shi.

Advertisement

Ta yi zargin amsar da Davido ya mayar mata kan hoton “ya yi ta ne cikin rashin girmamawa da ɓacin rai”.

Tiwa ta yi zargin Davido ya riƙa aikamata mutane Legas su jamata kunne “ta bi a hankali” wanda ta ce “hakan ya saɓa al’ada” kuma “barazana ce ga ‘yancinta na rayuwa, da mutuncinta”.

Har yanzu dai Davido bai ce komai ba kan wannan zargi.

Advertisement

Duka taurarin biyu dai sun yanke ƙawancen da ke tsakaninsu a Instagram.

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *