Connect with us

Politics

Ba na neman takarar shugabancin Jamiyyar APC – Yahaya Bello

Published

on

DAGA MUHAMMAD BASHIR MUSA 

Tsohon gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya ce yana biyayya ga jagorancin Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta Nijeriya.

Sakon Yahaya Bello na zuwa ne a lokacin da ake ta yaɗa batun cewa yana neman takarar jam’iyyar kuma za a yi taron zaɓen sabon shugaban APC din nan ba da jimawa ba.

Advertisement

FAƊA DA WAN ƘARFI: Dala ta lollotsa wa Naira kumatu, ta gaggaɓe mata haƙoran gaba a kasuwar ƴan canji

A sanarwar da ofishin watsa labaran Yahaya Bello ya fitar a ranar Talata da marece, ya ce “Muna sane da yadda wasu bata gari ke yunkurin kawo rudani a cikin shugabancin jam’iyyar APC. Wannan aiki ne na wasu jiga-jigan ‘yan adawa da wasu masu zagon kasa a cikin jam’iyyar.”

A cikin makon nan an yi ta yaɗa batun cewa nan ba da jimawa ba APC za ta yi taron zaben sabon shugaban jam’iyya, kuma Yahaya Bello za a bai wa shugabancin, ina har ake yada fastocinsa da nufin hakan.

Sai dai sanarwar ta ce “A wani bangare na zancen da ake watsawa har da yada hotunan yakin neman zabe dauke da hoton Alhaji Yahaya Bello, CON, tsohon gwamnan jihar Kogi, ana cewa ya fito takarar shugaban jam’iyyar APC na kasa. Labarin ƙage ne, ƙarya kuma ya kamata a yi watsi da shi.”

Advertisement

Yahaya Bello, wanda ya sauka daga mukamin gwamnan Kogi a makon da ya wuce bayan ƙarewar wa’adinsa, ya ce jam’iyyarsu ta APC ba ta da wani shiri na gudanar da babban taro ko zaben sabon shugaba, don haka babu wata fa’ida ta yada fastocin neman ko wane irin shugabanci a jam’iyya.

“Alhaji Yahaya Bello bai bai wa kowa izinin yada wata fosta a madadinsa ba domin ya kasance mai biyayya ga jam’iyya mai kishin jagorancin shugaban jam’iyyar na kasa, mai girma Gwamna Dr Abdullahi Ganduje.”

Dama an daɗe ana yaɗa batun cewa shugabancin jam’iyyar APC na shiyyar Arewa ta Tsakiyar Nijeriya ne a wannan karon, amma babu wani tabbacin hakan da aka ji daga wajen jam’iyyar.

Advertisement

A ƙarshe sanarwar ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da “ƙaryar da jama’a ke ta yaɗawa da fastoci don haifar da rashin gaskiya.”

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *