Connect with us

News

Aliko Dangote ya yi alkawarin tallafa wa Kano a fannin lafiya da taimakon marasa galihu

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka Alhaji Aliko Dangote ya yi alkawarin tallafa wa manufofin zamantakewa da shirin ci gaban ɗan’adam na gwamnatin Jihar Kano, da nufin rage ɗawainiyar tattalin arziki da ta yi wa jihar katutu.

Advertisement

Dangote ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da ya gana da Gwamna Abba Kabir Yusuf a gidan gwamnatin Jihar Kano, a ranar Juma’a, inda ya ce ya yi amanna talaka na cikin ƙunci kan halin da ake ciki na hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya.

Za A Bude Shafin Baiwa Daliban Nigeria Rancen Kudi A Ranar 21 Ga Watan Fabrairu

Attajirin ya ce ya so yin wannan ziyara tun da jimawa amma yawan tafiye-tafiyensa suka sa sai yanzu ya zo.

Dangote ya yi alkawarin tallafa wa Kano don inganta kiwon lafiya da ilimi da karfafa wa masu karamin karfi da ke gwagwarmayar rayuwa, kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar bayan ganawar ta ce.

Advertisement

“Da farko dai mun zo nan ne don mu taya ku murnar nasarar da kuka samu a Kotun Ƙoli, ina so in tabbatar muku da goyon bayanmu a tsawon mulkinku, watakila ba shekara hudu kawai ba har amma shekaru takwas.

Dangote wanda ya ce Kano gida ne a wajensa, duk da cewa mai gabatarwa a wajen taron ya bayyana shi a matsayin baƙar fatan da ya fi kuɗi a duniya, ya ce “Ni naku ne don haka koyaushe za ku iya kira na don hadin kai kan yadda za mu ciyar da Kano gaba.”

“Kuma a ci gaba da gaske muna bukatar ganin yadda za mu bunkasa fannonin kiwon lafiya da ilimi da ƙarfafa wa gwamnati, da ta yadda za mu taimaka wa gwamnati domin gwamnati ba za ta iya yin komai ita kadai ba”.

Advertisement

Dangote ya ci gaba da shaida wa Gwamna Abba cewa “Akwai haƙƙin mutane a kanku kuma a yanzu jama’a na cikin matsi. Don haka a yanzu ku ne za ku zama majinginar mutane mu kuma za mu taya ku ji da su.

“Don haka ku tabbata cewa za mu ba ku goyon baya kuma za mu goyi bayan gwamnatinku, kuma muna so mu gaya muku cewa za mu ci gaba da yi muku addu’ar samun nasara domin nasararku tamu ce.

 

Advertisement

       BAYANIN ABBA K YUSUF

A nasa bangaren, Gwamna Yusuf Yusuf ya nemi goyon bayan attajirin kan kafa cibiyar samar da wutar lantarki mai zaman kanta domin farfado da masana’antun da suka lalace da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar.

Hakazalika, Gwamnan ya shaida wa Dangote Kano cewa yana matukar bukatar a kafa asibitin masu cutar sikila a jihar domin samar da magunguna kyauta ga marasa lafiya.

Advertisement

Baya ga haka, sanarwar ta ce Abba Gida-Gida ya roƙi hamshaƙin ɗan kasuwan cewa “ka daure ka kammala manyan ayyukan da gidauniyarka ta Dangote ta ƙaddamar wadanda suka hada da sashen gaggawa da dakin tiyata da sashen mata masu juna biyu da na yara duk a Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhamnad.”

 

TRT Afrika

Advertisement
Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *