Connect with us

News

Yan Majalisa sun manta da matsalar tsaro da ta tsadar rayuwa, sun haƙiƙice kan yi wa ƙungiyoyin kishin jama’a takunkumi da dabaibayi.

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Bayan ‘yan Majalisar Tarayya sun shafe hutun kwanaki 30 a gida, tun daga tafiya Kirsimeti da Sabuwar Shekara, to sun dawo Abuja daidai lokacin da ‘yan Najeriya suka fi ɗanɗana raɗaɗin tsadar rayuwa da tsadar farashin kayan abinci wanda ba a taɓa samun kamar sa ba.

Advertisement

Abin mamaki, maimakon su maida hankali wajen abin da ya fi damun ‘yan Najeriya, wato tsadar rayuwa da matsalar tsaro, sai suka ɗibge suka haƙiƙice kan ƙudirin dokar yi wa ƙungiyoyin kishin jama’a (NGO) da (CSO) takunkumi da dabaibayi.

Aliko Dangote ya yi alkawarin tallafa wa Kano a fannin lafiya da taimakon marasa galihu

Sun fa koma Majalisa lokacin da ‘yan bindiga suka hana mazauna yankunan babban birnin tarayya, FCT Abuja da kewaye barci mai nauyi. Amma duk wannan ba ya gaban su, abin da ya fi damun su shi ne hayaniya da kwakwazon jayayya kan daƙile kaifin Ƙungiyoyin da ba na Gwamnati ba, wato NGO da CSO.

Premium Times ta ruwaito cewa Ɗan Majalisa Sada Soli, ɗan APC daga Jibiya, ƙaramar hukumar da ‘yan bindiga suka taso gaba a yanzu haka su na ragargazar kisan mutane da kama su kamar kaji ana yin garkuwa da su, ya manta da abin da ke faruwa a yankin mahaifar sa, sai ya gabatar da ƙudirin taƙaita NGOs. Kuma dama shi ne mai ƙudirin.

Advertisement

Wakilan nan fa sun tafi hutu Dala 1 ta na Naira 1,193 a kasuwar ‘yan canji. Sun koma majalisa Dala ta na 1,500. Amma duk wannan bai dame su ba. Abin da ke gaban su shi ne rage ƙarfin NGOs da CSOs.

Ai kuwa tuni talakawa sun fara zabga masu baƙaƙen kalamai a kafafen sada zumunta. Wasu na ce masu “ɗibgaggu”, wasu na ce masu “wakilan wasan gauta.” Wasu ma ce masu suke yi, “wakilan aljifan su da iyalan su.”

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa idan aka dubi matsalar rashin tsaro, da yawan waɗanda suka tafi hutun Kirsimeti da Sabuwar Shekara, ‘yan bindiga sun tare su. An kashe wasu, an yi garkuwa da wasu. Amma duk ‘yan Majalisa sun kauda ido. An kama iyakan magidanci a Abuja, an kashe biyu, har sai da ta kai tsohon Minista Ali Fantami fitowa soshiyal midiya ya na neman taimakon yadda za haɗa kuɗin karɓar fansar su.

Advertisement

Wannan duk ba ya gaban su. Haka yadda ‘yan bindiga ke fafarar Katsinawa a yankunan Batsari, Jibiya, Safana da sauran jihohi irin su Zamfara, Neja, Benuwai da rikicin kashe-kashen Filato duk bai dame su ba. Hankalin su na kan ƙudirin karya lagon NGOs da CSO, wato Civil Society Organizations.

Sada Soli, wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Majalisar Arewa-maso-Yamma, tun cikin Majalisar zangon 2019 zuwa 2023 ya fara haƙilon neman amincewa da ƙudirin, amma aka yi watsi da shi, saboda ‘yan Najeriya sun ragargaji ƙudirin. Har sai da ta kai an yi zanga-zanga zuwa Majalisar Tarayya, ana yi wa ƙudirin tofin Allah-tsine. Yanzu kuma shi ne ya sake tado da maganar.

Yanzu ɗin ma tuni ‘yan Najeriya sun fara dira kan sa, ana yi masa wankin-babban-bargo, shi da ƙudirin nasa.

Advertisement

Cikin masu ragargazar majalisa har da Chido Onumah, Shugaban AFRICMIL, wanda ya ce “ƙudirin ya na da hatsari da ban-tsoro.”

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *