Connect with us

News

Gobara Ta Ƙone Ofishin ‘Yan Sanda A Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce gobara ta kone ofishin ‘yan sanda reshen karamar hukumar Nasarawa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hussaini Gumel, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Kano ranar Litinin cewa lamarin ya faru ne da safiyar ranar Litinin.

Advertisement

‘’Da misalin karfe 05.45 na safe ofishin ‘yan sanda ya kama da gobara ya kone wani bangare na ginin ofishin.

”Wannan ya faru duk da irin gaggawar daukar matakai da Hukumar kashe gobara ta jihar ta dauka,” cewarsa.

Gumel ya ce ana ci gaba da bincike don gano musabbabin tashin gobarar.

Advertisement

‘’An killace yankin don hana masu shiga kallo da bata-gari shiga wurin, makamai da alburusai da ke ofishin suna suna nan a killace.

“A yanzu haka jami’in ‘yan sandan na tantance wasu takardu da abin ya shafa,” inji Kwamishina.

 

Advertisement

LEADERSHIP 

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *