Connect with us

Entertainment

Cikakken Dalilin da ya sa Kotu ta tura Murja Kunya asibitin masu tabin hankali 

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kotu da ke zama a birnin Kano ta bayar da umarnin tura Murja Kunya zuwa asibitin masu taɓin hankali domin duba lafiyar ƙaƙwalwarta.

Mai magana da yawun kotunan jihar Kano, Babajibo Ibrahim ne ya tabbatar wa BBC HAUSA hakan bayan zaman kotun da aka yi ranar Talata.

Advertisement

Hukumar Hisbah A Zamfara Ta Hana ‘Ƙauye Day’ Da Sauran Bukukuwan Aure Da Ba Su Cancanta Ba A Jihar

Babajibo ya ce yanayin da Murja ke ciki da kyanayin kamanninta da maganganun da take faɗa sun nuna cewa ba ta cikin hali irin na mutum mai cikakken hankali.

” Wannan ne dalilin da ya sa alƙalin ya buƙaci a tura Murja zuwa asibitin masu lalurar ƙwaƙwalwa har zuwa ranar 20 ga watan biyar, 2024.”

Hukumar Hizba ta jihar Kano ce ta kama Murja Kunya tare da miƙa ta ga jami’an tsaro bisa zargin ta da laifukan da suka shafi baɗala a shafukan sada zumunta.

Advertisement

Kwamandan hukumar ta Hizba a jihar, Sheikh Ibrahim Daurawa ya ce tuhume-tuhumen da ake yi wa Murja Kunya sun haɗa da: Razana al’umma, ayyukan baɗala, tayar da hatsaniya, tayar da hankalin al’umma, kawo ɓata-gari cikin unguwa da kuma iƙirarin cewa ita ce shugaban karuwai da ƴan kwalta.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply