Connect with us

Sports

An raba gari tsakanin Super Eagles da kocinta Jose Peseiro

Published

on

Jose Peseiro
Spread the love

Kocin Najeriya Jose Peseiro ya sanar da kammala aikinsa da tawagar Super Eagles.

Kocin ɗan asalin Portugal ya bayyana hakan ne a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter a ranar Juma’a.

Murabus Din Daurawa Ta Tayar Da Kura A Kano

Advertisement

“A jiya muka kawo ƙarshen kwantaragin da ake tsakanina da Hukumar Kwallon ƙafa ta Najeriya NFF.”

“Abin farinciki da alfahari ne koyar da tawagar Super Eagles. Watanni 22 kenan da muka kwashe muna wannan sadaukarwa da mutakuar sha’awar aikin. Muna jin mun yi abin da ya kamata,” kamar yadda kocin ya rubuta.

Ya ce yana so ya nuna godiyarsa ga tsohon shugaban hukumar NFF Amaju Pinnick da kuma na yanzu Ibrahim Gusau da Sakataren NFF Mohammed Sanusi da duka ma’aikatan hukumar da duka ‘yan wasan, wadanda duka muka yi zaman kirki da su.

Advertisement

Jose Peseiro ya fara aiki ne da Spuer Eagles a watan Mayun 2022 bayan Augustine Eguavoen ya gaza samun tikitin zuwa gasar Kofin Duniya.

Peseiro ya bar aikin Venezuela ne a wancan lokacin, kuma an ta nuna shakku kan cancantarsa ganin ba shi da wani tarihin azo a gani.

Kocin dai shi ne ya kai Super Eagles wasan ƙarshe a gasar Cin Kofin ƙasashen Nahiyar Afrika, wanda ta sha kashi a hannun Ivory Coast da ci 1-0 babu ko ɗaya.

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply