Connect with us

News

Ɗaliban Kuriga 137 Muka Yi Nasarar Kuɓutarwa A Zamfara, Ba Ɗalibai 287 Ba— Sojoji

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hedikwatar tsaron Nijeriya, ta bayyana cewa dakarunta da hadin guiwar sauran hukumomin tsaro sun ceto ‘yan makaranta 137 da aka sace a Kuriga da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Daraktan yada labarai na rundunar, Manjo Janar Edward Buba, ya ce yaran da aka ceto sun hada da mata 76 da maza 61 da safiyar Lahadi 24 ga Maris, 2024, a wani wuri a jihar Zamfara.

Advertisement

Ranar Tarin Fuka: Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Da Shirye-shiryen Kawo Karshen Cutar Tarin Fuka A Jihar —Dr Labaran

Idan ba a manta ba Jaridar LEADERSHIP HAUSA a ranar 7 ga Maris, 2024 ta rawaito muku yadda wasu ‘yan ta’adda suka kai hari makarantar LEA Kuriga, karamar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da ‘yan makaranta 287.

Gwamnatin tarayya dai ta umurci sojoji da su tabbatar an dawo da yaran makaranta lafiya.

A baya LEADERSHIP ta kawo rahoto kan cewa an kubutar da daliban, a cewar gwamnan jihar Uba Sani, wanda ya sanar da farko game da ceto yaran ba tare da bayyana adadin wadanda abin ya shafa ba a safiyar yau Lahadi.

Advertisement

Sai dai a cewar sanarwar ta hedikwatar tsaron Nijeriya ta cfurta ya saba da alkaluman farko na adadin daliban da sojojin suka ce sun yi nasarar kubutar da su.

“A ranar Lahadi, 24 ga Maris, 2024, sojojin da ke aiki tare daw hadin guiwar wasu hukumomi sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

“Wadanda aka yi garkuwa da su daga makarantar da ke Kuriga a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Advertisement

“Dalibai 137 da aka yi garkuwa da su sun hada da mata 76 da maza 61, an ceto su ne a jihar Zamfara kuma za a mika su ga gwamnatin jihar Kaduna,” inji Manjo Janar Buba.

Rundunar sojin ta ce za a ci gaba da kokarin har sai an gano ragowar mutanen da aka yi garkuwa da su da tabbatar da an kama ’yan ta’addar an yi musu an gurfanar da su gaban shari’a.

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply