Connect with us

News

Hukumar NAHCON Ta Mayar Da Kuɗin Hajjin Bana Kusan Naira Miliyan 7

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta buƙaci maniyyatan bana da su yi gaggawar biyan N1,918,032.91 ƙari a kan kuɗin kujerar Hajjin bana.

Hukumar ta buƙaci maniyyatan da ke son sauke farali a bana kuma suka riga da bayar da kuɗin ajiya da su gaggauta cika kuɗin daga yanzu zuwa ƙarfe 11:59 na daren 28 ga Maris, 2024.

Advertisement

Mutum Huɗu Sun Rasa Ransu A Tirmitsitsin Karɓar Zakka A Jihar Bauchi

Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar alhazan, Farima Sanda Usara ta fitar a Yammacin wannan Lahadin.

Hajiya Usara ta ce hukumar za ta rufe karɓar cikon kuɗin ne a ranar 29 ga watan Maris, kuma daga wannan lokaci babu wani maniyyaci da za su saurara matuƙar bai biya kuɗin kafin lokacin ba.

A yanzu dai bayan wannan ƙarin, duk wani maniyyaci zai biya kusan Naira miliyan bakwai matuƙar yana son sauke farali a bana.

Advertisement

Sanarwar ta ce sabbin waɗanda suke da sha’awar sayen kujerar daga jihohin Adamawa, Borno da Yobe, za su biya Naira miliyan 8,225,467.74 yayin da waɗanda suka fito daga sauran yankunan Arewa za su biya Naira 8,254,464.74.

Haka kuma, sabbin waɗanda ke da sha’awar sauke faralin da suka fito daga yankunan Kudu, za su biya Naira miliyan 8,454,464.74, kuma duk a tsukukun wa’adin rufe karɓar kuɗin da Hukumar NAHCON ta bayar.

Ana iya tuna cewa, tun a watan Fabarairun da ya gabata ne hukumar alhazan ta ƙayyade kusan naira miliyan biyar a matsayin kuɗin kuejrar hajjin bana.

Advertisement

Aminiya ta ruwaito cewa tun bayan lokacin, hukumar ta soma tababar ƙara wa maniyyatan kuɗi a dalilin tsadar Dala da ke neman hana yi wa maniyyatan dawainiyar da aka saba yi musu ta masauki, abinci da makamantansu.

A wancan lokacin dai, NAHCON ta buƙaci maniyyata daga jihohin Kudancin Najeriya su biya naira miliyan 4,899,000, yayin da maniyyatan Arewa za su biya naira miliyan 4,699,000.

Sai kuma maniyyatan jihohin Yobe da Maiduguri da aka ƙayyade kuɗin kujerarsu a kan naira miliyan 4,679,000.

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply