Connect with us

News

Muhimmancin ciyarwa da ba da sadaka a watan Ramadan

Published

on

Spread the love

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Watan azumi dai lokaci ne da Musulmi ke zage damtse wajen yin ibada da nufin samun rabauta daga Allah SWT.

Sheikh Tukur Al-Manar, malamin addini da ke jihar Kaduna, ya ce ciyarwa na ɗaya daga cikin manyan ayyuka ayyukan da ke ƙara yawan ladan mai azumi, wanda muhimmancinsa ba ya misaltuwa.

Advertisement

Hukumar NDLEA Ta Tarwatsa Wasu Kungiyoyin Ta’ammuli Da Hodar Iblis A Abuja Da Kano

Ya ce ko da ba a kwanaki na Ramadan ba, Allah Ya kwaɗaitar da a ciyar.

Ya kuma ce Manzon Allah S.A.W shi ma ya karfafa wa mutane wajen ganin sun ciyar da marasa karfi.

Malamin ya ce ayoyin Al-Kur’ani da suka zo kan ciyarwa ba sa misaltuwa.

Advertisement

“Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce ku ciyar daga abin da muka azurtaku daga ƙasa, ku ciyar daga abin da muka damƙa a hannunku, ku ciyar da tsarkakke mai kyau wanda aka samo shi ta hanya mai nagarta,” in ji Sheik Al-Manar.

Malamin ya ce Manzon Allah shi ne wanda ya fi kowa kyauta, kuma ya fi yin haka a lokacin azumin Ramadana.

Ya kuma ce Allah Ya zargi waɗanda ba sa ciyarwa kuma ba sa taimakawa saboda hakan ba daidai ba ne.

Advertisement

Nau’in abincin da ya kamata a ciyar da mai azumi

Ya ce ba a kayyade wani nau’in abinci da aka ce shi ne ya kamata a ciyar da mai azumi ba, inda ya ce a ciyar da irin nau’in abincin da jama’a suka fi dogaro da shi.

“Nau’in abinci na ƙasashe ya bambanta, kamar Larabawa idan aka samu dabino suna sarrafa shi su yi kus-kus da shi. Idan ka bai wa mutanen mu tulin dabino ba su san yanda za su sarrafa shi ba,” in ji Sheikh Al-Manar.

Advertisement

Malamin ya ce a lokacin Ramadan kowane irin nau’in ibada ninƙa shi ake yi saboda Allah Yana ninƙa ladan ibadar.

“Manzon Allah S.AW. ya ce idan ka ciyar da mai azumi daga abincinka, za a ba ka kwatankwacin ladan shi mai azumin ba tare da an rage na shi ba.

“Mu a nan za mu iya ciyarwa da alkama, masara, gero, dawa, maiwa, garin kwake da tuwon alabo,” in ji Malamin.

Advertisement

Ya ce Allah ya bar wa kansa sanin yawan ladan da yake bai wa azumi saboda falalar watan.

BBC  ta ruwaito cewa Sheikh Tukur Al-Manar ya ce Allah bai ce mutum ya ɗebi hakkin wani ko ɗauka daga asusun gwamnati ba don kawai yana son ciyarwa.

“Kowane irin ciyarwa za ka yi idan ba hakkinka ba ne Allah ba zai karɓa ba idan ba ta hanyar halal ka samu kuɗinka ba,” in ji Malamin.

Advertisement

Ya ce mutum ya tsaya cikin waɗanda ke burin aikata alkhairi ko da ba su da shi saboda Allah zai ba su ladan niyyar aikata alkahiri da suka yi ko da ba su yi ba.

Ya ce waɗanda ba su da halin ciyarwa su yi ta addu’ar Allah ya ba su damar samu don su ciyar.

Malamin ya ce su kuma riƙa yi wa masu ciyarwa addu’ar Allah ya karɓa musu irin alkhairin da suke yi.

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply