Connect with us

News

Sabon Rikici Tsakanin Hausawa Da Fulani Ya Yi Sanadin Mutuwar  Rayuka 4 A Sokoto

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Tashin hankali tsakanin al’ummomin Hausawa da Fulani a Najeriya na ci gaba da kawo cikas ga kokarin samar da zaman lafiya musamman a yankunan arewacin kasar.

Muryar Amurka ta ruwaito cewa yanzu haka ana zaman dar dar tsakanin Hausawa da Fulani a karamar hukumar Gudu ta jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya, inda riciki tsakaninsu ya lakume rayukan mutane hudu.

Advertisement

Tun kafin wannan lokaci da rashin tsaro ya dagula al’amura a Najeriya, rikici tsakanin Hausawa manoma da Fulani makiyaya ya jima yana mayar da hannun agogo baya ga samar da zaman lafiya, duk da kokarin da mahukunta ke cewa suna yi wajen hada hankulan kabilun biyu.

Irin wannan rikici ne ya barke tsakanin Hausawa da Fulani a kauyen Jimjimi da ke kusa da Jamhuriyar Nijar, a karamar hukumar Gudu ta jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Rikicin ya tashi ne sanadiyyar amfani da wani gandu, wanda Huasawa da Fulanin duk suna amfani da shi, don yin noma da kiwo.

Advertisement

Daya daga cikin Fulanin ya bayyana cewa ranar Laraba ta wannan mako Hausawa sun je aikin daji, bayan sun dawo gida sai suka tarar wasu daga cikin su ba su dawo ba, sai suka yi zargin Fulani da hannu ga rashin dawowar ‘yan uwansu, kuma su ka yi takakka zuwa rugar Fulanin suka bayyana korafinsu.

A cewar Fulanin, ganin haka ya sa Ardon Rugar ya umurci kowa ya fice daga rugar don tsammanin abinda ka iya faruwa mummuna, kuma suka kai batun ga karamar hukuma domin a shiga tsakaninsu, amma kwatsam cikin dare sai ga Hausawa sun afka wa garin suka kona gidaje da runbunan abinci, suka tarwatsa garin wasu mutane ma sun rasa rayukkansu.

Kantoman karamar hukumar ta Gudu, Umma Maikano, ya ce lokacin da Hausawa suka je daji sai suka tarar ba Fulani ko daya da ya zo dajin suna aiki daga nan sai suka ji ana harbe-harbe.

Advertisement

Ya ce wasu mutane ne da bindiga suke harbin Hausawa har suka kashe mutum biyu, washegari ya tura motar sojoji da ‘yan sanda suka je kwantar da fitinar, sai Hausawa suka bi sawun masu bindigar suka je har rugar Fulanin suka kone bukka daya da mashin a ciki, da wani wuri inda Fulani ke zama, amma dai daga baya Sojoji sun dakatar da rigimar.

To sai dai Fulanin sun ce ba su ne suka harbi, Hausawan ba, basu ma san ko su waye ba, kawai dai Hausawan sun so su dauki mataki ne a kan Ruggar ta su, suka yi musu wannan aika-aika.

Shi kuwa shugaban karamar hukumar ya ce wasu mutane kawai suna furta kalaman da suke son furtawa ne, ba don sun san hakikanin abin da ke faruwa ba ne, kuma akasarinsu ba ma garin suke zaune ba.

Advertisement

Ya ce shi baya goyon bayan kowa daga cikin bangarorin, muradin sa yi wa kowa adalci a kuma samu zaman lafiya, amma tabbas an kashe Hausawa biyu an kashe Fulani biyu amma maganar kone gari ba gaskiya ba ne, an dai kone bukka da mashin a ciki da kuma wani mazaunin Fulanin.

Yanzu haka dai ana kan tattaunawa don yin sulhu tsakanin bangarorin biyu karkashin jagorancin Kantoman.

Na tuntubi Rundunar ‘yan sandan Najeriya akan wannan lamarin, sai dai kakakinta a Sakkwato, ASP Ahmad Rufa’i, ya ce min zai bincika yadda lamarin yake.

Advertisement

Ko a shekarar da ta gabata an samu irin wadannan rikice-rikicen a kananan hukumomin Binj da Tangaza inda aka yi asarar rayuka masu yawa, baya ga wasu makamantansu da ake samu a wasu sassan Najeriya.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply