Connect with us

Politics

Daga kurkuku ya zamo shugaba mafi ƙarancin shekaru a Afirka

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Mutane ƙalilan ne suka san shi a shekarar da ta wuce, amma yanzu ya shirya zama shugaban ƙasa.

Tashen ban al’ajabi na Bassirou Diomaye Faye, wani lokaci ne mai cike da hawa da gangara a tarihin siyasar Senegal, da kuma ya zo da mamaki ga mutane da dama.

Advertisement

Muna sane da tsare ɗanƙasarmu ma’aikacin Binance a Najeriya – Amurka

Watannin da ya shafe tsare a gidan yari tare da babban abokin siyasarsa kuma ubangidansa Ousmane Sonko sun zo ƙarshe a yayin da ya rage mako ɗaya a yi zaɓen shugaban ƙasar.

A yanzu Mai gaskiya, kamar yadda ake yi masa laƙabi, zai iya fara aiki kan manyan sauye-sauyen da ya yi alƙawarin kawowa a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Advertisement

Mai tabbatar da bin tsari” da “ƙas-ƙas da kai” su ne kalmomin da aka fi amfani da su wajen bayyana jami’in karɓar harajin, wanda ke bikin cikarsa shekara 44 da haihuwa a ranar Litinin.

Mallam Faye cikin murna yakan tuna rayuwar ƙuruciyarsa ta ƙauye a Ndiaganiao, inda ya ce yakan kai ziyara a duk ranar Lahadi don yin aiki a gona.

Ƙaunarsa da darajar da yake bai wa rayuwar mutanen karkara sun dace da zuzzurfan rashin amincewarsa da manyan ƙasa a Senegal da kuma tsarin siyasar da aka saba da ita.

Advertisement

“Bai taɓa riƙe muƙamin minista ba, kuma shi ba gogaggen jami’in gwamnati ba ne don haka masu suka suke tuhumar rashin gogewarsa,” kamar yadda mai sharhi Alioune Tine ya faɗa wa BBC.

“Sai dai, fahimtar Faye, jami’an da suka tafiyar da harkokin mulkin ƙasar tun daga 1960 sun tafka manya-manyan kura-kurai.”

Yaƙi da fatara da rashin adalci da kuma cin hanci na cikin manyan manufofin Mallam Faye. Da yake aiki a Baitulmali, shi da Ousmane Sonko sun kafa wata kungiyar ko-ta-kwana don tunkarar masu cin hanci da rashawa.

Yarjeniyoyin haƙar iskar gas da man fetur da kuma na tsaro jazaman ne sai an sake cimma matsaya a kan su don su biya muradan al’ummar Senegal, in ji Mallam Faye.

Advertisement

Yana ƙoƙarin kawo wani zamani na “gwamnati mai cikakken iko da “birkita al’amura” saɓanin yadda aka saba yi a baya, kamar yadda ya faɗa wa masu zaɓe, da kuma musamman haƙiƙanin alaƙarsu da Faransa.

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar na Senegal ya ce zai yi watsi da kuɗin saifa na Faransa da ake yawan sukar lamiri, wadda ake kwatanta darajarta da yuro sannan take samun goyon bayan Faransa, tsohuwar uwargijiyar mulkin mallakar Senegal.

Mallam Faye dai yana son maye gurbin saifa da wani sabon kuɗin Senegal ko na yankin Afirka ta Yamma, ko da yake hakan ba abu ne mai sauƙi ba.

Advertisement

“Zai ci karo da ƙalubalen haƙiƙanin al’amura kamar na kasafin kuɗin a farkon farawa… Sai dai na lura shi mutum ne mai ɗumbin buri,” tsohuwar Firaminista Aminata Toure wadda ta yi aiki a ƙarƙashin shugaba mai barin gado Macky Sall ta bayyana wa BBC.

Ƙarfafa ‘yancin cin gashin kai ga ɓangaren shari’a da samar da ayyuka ga ɗumbin matasan Senegal su ma suna cikin manyan manufofin Mallam Faye – dukkansu biyun dai “ba su samu wata kyakkyawar kulawa ba daga Shugaba Sall, alhakin hakan kuma sai da ya kama shi”, Aminata Toure ta ƙara da cewa.

Ba ita ce kaɗai babbar ‘yar siyasa da ta mara baya ga matashin ɗan shekara 44 ba – tsohon shugaban ƙasar Abdoulaye Wade shi ma ya yi hakan kwana biyu kacal kafin zaɓen ranar Lahadi.

Advertisement

Wani gagarumin sauyin rayuwa ne ga Mallam Faye bayan ya shafe wata 11 da ya wuce tsare a gidan yari bisa tuhume-tuhumen bore da kuma shekaru da dama kafin nan a ƙarƙashin siyasar abokiyar tafiyarsa.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply