Connect with us

News

Maniyyatan Najeriya Sun Nemi Hukumar NAHCON Ta Mayar Musu Kudadensu

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Maniyyatan Najeriya, sun bukaci Hukumar Alhazan kasar NAHCON da ta mayar musu da kudadensu na aikin hajjin da suka biya, biyo bayan karin kusan naira miliyan biyu da aka musu na tafiya kasa mai tsarki.

Wannan na zuwa ne bayan da kungiyoyin gamayyar kungiyoyin farar hula na kasar, suka yi kira ga shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu da ya ceto maniyyatan kasar, la’akari da halin matsin tattalin arzikin da ake ciki.

Advertisement

Karyewar babbar gadar Baltimore ta gigita Amurka

A ranar Lahadi ne, NAHCON ta sanar da cewa an kara sama da naira miliyan daya da dubu 900 na kudin aikin hajjin bana ga maniyyatan da ke shirin tafiya kasar Saudiyya sauke faralli, saboda matsalar karyewar darajar kudin kasar.

Darajar kudin Najeriya ta fuskanci koma baya a kan farashin dala a ‘yan kwanakin nan, kodayake a halin yanzu an fara ganin farfadowar darajar kudin kasar, sakamakon matakin da babban bankin CBN ya ce ya fara dauka na shawo kan matsalar.

A ranar 29 ga Maris ne, NAHCON ta ce, za ta rufe karbar kudin maniyyata, kamar yadda mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara ta tabbatar a wata sanarwa.

Advertisement

Bincike daga Arewaci zuwa Kudancin kasar ya tabbatar da cewa, kalilan na maniyyata ne suka shirya biyan karin kudin da aka musu, yayin da da dama daga cikinsu suka hau kujerar naki, tare da neman hukumomin jin dadin alhazan jihohinsu su mayar musu da kudadensu.

RFI

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply