Connect with us

News

Yanzu-yanzu: Gwamnatin Tarraya Ta Ayyana Juma’a Da Litinin A Matsayin Ranakun Hutu 

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranar 29 ga Maris da 1 ga Afrilu a matsayin ranakun hutun bukukuwan Good Friday da Easter Monday na bana.

Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, shi ne ya bayyana haka a madadin Gwamnatin Tarayya a ranar Laraba.

Advertisement

Sojoji Sun Ga Bayan Shahararren Ɗan Bindigar Nan Dogo Gide

Ya bayyana hakan ne a ciki wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Babbar Sakatariyar Ma’aikatar, Aishetu Ndayako.

Tunji-ojo ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga mabiya addinin Kirista da ma ‘yan ƙasa baki ɗaya kan a yi koyi da karantarwa Yesu kamar yadda ya nunar a halin rayuwarsa.

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply