Connect with us

News

Dinkin Sallah: Dalilan Da Yasa Teloli Ke Saba Alkawari

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Wata tela ta bayyana dalilan da ke sanya teloli ba sa cika wa masu ba su dinki alkawari, musamman a lokacin Karamar Sallah.

Khadija Naseer da ke dinki a Unguwa Uku dake Jihar Kano, Ta ce rashin tsari ke sa teloli karbar dinkuna fiye da kima a lokacin azumi saboda yawan kawo dinkunan da ake yi a lokacin.

Advertisement

Yanzu-yanzu: Gwamnatin Tarraya Ta Ayyana Juma’a Da Litinin A Matsayin Ranakun Hutu 

Khadija ta shidawa wakilin jaridar Inda Ranka cewa sau tari za ka ga telan da ya dade bai sami dinki ba, sai a irin wannan lokaci, za ka ga ana ta kawo mishi.

“Sau da yawa sai tela ya manta da irin dawainiyar da zai yi, kafin ya farga sai dinkunan da ya karba sa fi kirfinsa.

“Wannan dalili ne ya sa ake samun rashin cika, alkawari daga wajen teloli,” a zo ana rikici da su a cewarta

Advertisement

JIN KUNYA

Khadija tela, ta bayyana cewa bayan haka, “Masu kawo dinki, idan ka ce aiki ya yi maka yawa, ba za ka sami damar yi ba;

“Wani ba zai yarda ba, wani kuma za ka samu akwai kunya a tsakani; don haka sai tela ya ji nauyin kin karba.

Advertisement

“Amma kamar ni, idan mutum ya kawo mini dinki, na gwammace mu yi fada da shi, kan ban karbi dinkinsa ba, da na karba mu zo muna fada a kan ban yi mishi ba.” inji Khadija

KAWO DINKI A MAKARE

Khadija Naseer ta yi bayanin cewa, “Halin da ake ciki a kasar nan ne ya sa masu dinki ba sa kawo dinki da wuri.

Advertisement

“Wani sai azumi ya zo karshe, sai Allah Ya kawo mishi wata hanya, ya samu ya sayi yadi ya kawo.

“Muna ganin wasu ba sa samun kayan ne da wuri, wasu kuma suna ta abinci ne, amma duk da haka wani idan ya samu kofa, sai ya je ya sayi kayan ya kawo.”

RASHIN SAMUN DINKI

Advertisement

Ta ce dangane da masu kawo dinki ba su samu ba, wasu idan ba su sami dinkin ba, sukan yi hakuri.

“Wani duk abin da za ka gaya mishi ba zai yi hakuri ba, sai dai a yi ta musayar maganganu, har a kai ga samun sabani.”

 

Advertisement

DALILAN DA NAKE CIKA ALKAWARI’

Ameerah wata tela ce ita ma a Unguwa Uku ta bayyana cewa ta bata samun matsala wajen cika wa mutane alkawari a dinkin da take yi.

Don haka tana da jama’a da dama daga wurare daban-daban da suke kawo mishi dinki.

Advertisement

Ta ce, dalili shi ne duk wanda ya kawo mata dinki, Takan fada mata gaskiya idan ba za ta sami damar yi ba.

Ta a shawarci teloli, kan duk abin da mutum ba zai iya ba, ya fito ya fadi gaskiya.

“Abin da zai iya ya karba, abin da ya san ba zai iya ba, kada ya karba,” inji Ameerah

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply