Connect with us

Uncategorized

Kotu ta ba da umarnin sakin mutum 313 da aka zarge su da ta’addanci a Borno – Hedikwatar Tsaro

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hedikwatar tsaro ta Nijeriya ta ce wata Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Borno ta bayar da umarnin sakin mutane akalla 313 da ake zargin ‘yan ta’adda ne da sojoji suka kama.

Kotun ta bayar da umarnin a sake su ne a ranar Alhamis saboda rashin shaidar da za a bi wajen ɗaure wadanda ake zargin bayan bincike.

Advertisement

Rumbun samar da hasken wutar lantarki na Nijeriya ya sake lalacewa.

Daraktan ayyukan yaɗa labarai na rundunar, Manjo Janar Buba Edward a yayin da yake yi wa manema labarai ƙarin haske a Abuja kan ayyukan sojojin, ya ce “a cikin wannan mako, a bisa bin umarnin kotu na Babbar Kotun Tarayya da ke Maiduguri, an saki mutum 313 da ake zargi da aikata laifukan da suka shafi ta’addanci.”

Ya kuma ba da tabbacin cewa sojoji za su bi umurnin kotu tare da miƙa wadanda ake zargi da aikata ta’addanci ga gwamnatin jihar.

“Kotu ta bayar da umarnin sakin nasu saboda neman shaida bayan kammala bincike da sauran wasu batutuwa. A bisa ga haka, za a miƙa su ga gwamnatin jihar Borno domin ci gaba da daukar mataki,” in ji kakakin rundunar, inda ya ƙara da cewa Ma’aikatar Shari’a da ma’aikatar shari’a ta tarayya ne suka gurfanar da su gaban kuliya.

Advertisement

Jaridar Ounch ta rawaito cewa ba wannan ne karo na farko da aka saki mutanen da ake zargi da ta’addanci ba saboda rashin shaida.

Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi (SAN), a ranar 4 ga watan Disamban 2023, ya ce daga cikin mutane 1,323 da ake tuhuma da aikata ta’addanci, 366 ne kawai aka samu da laifi.

Ya ce an saki 896 saboda rashin isassun hujjoji.

Advertisement

 

TRT Afrika

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply