Connect with us

News

An Kama Wani Matashi Dan Shekara 20 Da Zargin Laifin Garkuwa Da Kuma Kashe Dan Jami’in Dan Sanda A Bauchi

Published

on

Spread the love

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta cafke wani da ake zargi da yin garkuwa da wani yaro dan shekara 12 mai suna Christopher Bala tare da kashe shi a garin Magama da ke karamar hukumar Gumau.

Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa anyi garkuwa da shi a ranar 21 ga Maris, 2024, a lokacin mahaifin yaron  yake bakin aiki, dan wani jami’in dan  sanda ne, ASP Bala Yarima na sashin Gumau.

Advertisement

Gwamna Uba Sani Yayi Tayin Bada Ilmi Kyauta Ga Daliban Kuriga Da Naira Milyan 10 Ga Iyalan Malamin Da Aka Kashe

Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil, ya fitar a ranar Alhamis, ta bayyana cewa rundunar ‘yan sandan ta samu kiran wayar da kan jama’a game da sace Christopher, inda nan take ta dauki matakin cafke wadanda suka aikata laifin.

Wanda ake zargin, Rabi’u Ibrahim, wanda aka gano a lokacin binciken farko, an ce ya amsa laifinsa.

Ya kuma yi ikirarin karbar kudin fansa N200,000 daga ASP Yarima.

Advertisement

Rahotanni sun ce Ibrahim ya amince ya shake Christopher ne saboda tsoron kada a gane shi, sannan ya binne gawar a wani kabari mara zurfi a tsaunin kauyen Bazale.

“Bayan bin tsarin da aka kafa, rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tono gawar mamacin. Wani bincike da aka gudanar a babban asibitin Toro ya tabbatar da Mutuwar a matsayin shakewa.

“Daga baya, an mayar da bincikenzuwa sashin binciken manyan laifuka domin gudanar da cikakken bincike, biyo bayan umarnin da kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar,” in ji sanarwar.

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply