Connect with us

News

Gwamna Uba Sani Yayi Tayin Bada Ilmi Kyauta Ga Daliban Kuriga Da Naira Milyan 10 Ga Iyalan Malamin Da Aka Kashe

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna yayi tayin bada ilmi kyauta ga daliban makarantar Kuriga da aka kubutar a karkashin gidauniyarsa.

Gwamnan ya kuma sha alwashin sake gina makarantun firamare dana sakandaren Kuriga tare da samawa al’ummar yankin kayayyakin more rayuwa.

Advertisement

Kotu ta ba da umarnin sakin mutum 313 da aka zarge su da ta’addanci a Borno – Hedikwatar Tsaro

A jawabinsa ga daliban gabanin tashinsu zuwa Kuriga a yau Alhamis, Gwamna Sani ya basu tabbacin cewar al’amarin yin garkuwa dasu ba zai shafin batun ilminsu ba, inda yace an tabbatar da ingantaccen tsaro ga al’ummar garin kuriga domin su cigaba da rayuwa cikin walwala da aminci.

“Na umarci gidauniyar uba sani wacce ta shafe fiye da shekaru 16 tana bada ilmi da lafiya kyauta, ta cigaba da kula dasu.

“Na kuma bada umarnin a gudanar da gyare-gyare a makarantu da garin kuriga, domin a wurina kuriga gari ne me son zaman lafiya a jihar Kaduna”.

Advertisement

Ya kuma sanarda gudunmowar Naira miliyan 10 ga iyalan Shed Mastan, Abubakar Isah daya mutu a hannun masu garkuwa da mutane, sa’annan yayi tayin daukar nauyin karatun ‘ya’yansa har izuwa matakin jami’a.

“Gwamnatin jihar Kaduna zata cigaba da tallafawa karatun ‘ya’yan malam abubakar. Kuma zamu tallafawa iyalansa da gudunmowar naira milyan 10 domin halin da suka tsinci kansu a ciki. Malam abubakar ya rasu ne sakamakon wata jinya da yake fama da ita. Muna rokon all.hya gafarta masa.

Saidai gwamnan ya ki yin karin haske game da yadda aka bi wajen kubutar da daliban, inda ya dage akan cewar bayanin bashi da mahimmanci.

Advertisement

A cewarsa, abinda keda mahimmanci shine gwamnati tayi nasarar dukkanin daliban ba tare da illata ko guda daga cikinsu ba.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply