Connect with us

News

Daliban Jami’ar Alqam  Sun Maka Makarantar A Kotu

Published

on

Spread the love

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Wasu daliban jami’ar nan mai zaman kanta da ke Katsina, Alqalam University, su uku sun garzaya kotu, inda suke neman da a tilasta wa jami’ar ta tura sunayensu a jerin matasa masu yi wa kasa hidima na NYSC.

Daliban sun je babbar kotun jihar Katsina ne bisa zargin da jami’ar ta yi musu na cewa ba su biya kudin rajistar zangunan karatu hudu ba a jami’ar.

Advertisement

Kwamitin Zaman Lafiya Na Jihar Kano Ya Yabawa Rundunar Yan Sanda Akan Kokarin Da Sukayi Na Kawo Zaman Lafiya A Dorayi

Daliban ‘yan gida daya, Hawwa’u Sani Barda, Rabi’atu Sani Barda da Hafsat Sani Barda sun samu takardar shaidar shiga jami’a ta ‘admission’ a zangon karatu na 2018/2019 da suka kammala a zangon karatu na 2022/2023.

DCL Hausa ta ruwaito cewa Daliban dai sun yi ikirarin cewa jami’ar ta ki ta tura sunayensu a shirin hidimta wa kasa na NYSC, bisa hujjar jami’ar cewa, daliban ba su biya kudaden rajistar karatu ba.

A lokacin zaman kotun, lauyan masu kara Muhammad Mukhtar Lawal ya ce wadanda ya ke karewa sun zo kotu ne domin neman hakkinsu kamar yadda kundin mulkin kasa na 1999 ya tanadar.

Advertisement

Mukhtar Lawal ya ce takardar ta nemi izinin kotu domin a duba wannan shari’a.

Bayan gabatar da karar, Alkalin kotun, Mai shari’a Abbas Bawale, ya ce ya kamata masu karar su shigar da bukatar kotu ta aike sammace ga jami’ar domin lauyoyinta suma su halarci zaman shari’ar.

Sai dai Mai Shari’a Abbas Bawale ya ba masu karar damar yin nazari sosai a kan wannan karar, inda aka basu wa’adun kara shigar da karar wadda ta hada da bukatar kotu ta aikawa jami’ar takardar sammace.

Advertisement

Ya ce bayan haka za a bi hanyoyin da suka dace don isar da sammacen, daga nan kuma kotu ta sanya ranar da za’a fara shari’ar.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply