Connect with us

News

Kasafin Kudi: Majalisar Dattawa Za Ta Duba Dakatarwar Da Aka Yi Wa Ningi – Akpabio

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana cewa majalisar za ta dawo da Sanata Abdul Ningi daga dakatarwar da aka yi masa na tsawon watanni uku.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a lokacin da ya isa wurin taron kungiyar ‘yan majalisar dokokin kasar a birnin Geneva na kasar Switzerland.

Advertisement

Sabuwar Amarya Ta Antaya Wa Angonta Ruwan Zafi Akan Waya

Akpabio ya ce nan ba da jimawa ba majalisar dattawa za ta sake duba dakatarwar da ta yi wa Ningi na tsawon watanni uku saboda ikirarin cewa an yi wa kasafin kudin shekarar 2024 cushin makudan kudade har naira tiriliyan 3.7.

DAILY POST ta ruwaito cewa Ningi a ranar Alhamis, a wata wasika da lauyansa, Femi Falana SAN ya rubuta, ya bukaci a mayar da shi Bakin aiki

Akpabio ya yi nuni da cewa duk da bai ga wasikar ba, za a warware matsalar

Advertisement

Ya ce: “Hukuncin majalisa ne. Har yanzu ban ga wasikar ba. Amma Sanata Ningi yana daya daga cikin mu.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply