Connect with us

News

Ƴan Sanda Sun Kama Mutumin Da Ya Daɓawa Ɗanuwansa Wuƙa Har Lahira.

Published

on

Spread the love

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta yi nasarar kama Isyaku Babale mai shekaru 30 wanda ke unguwar Dawaki da ke cikin birnin Bauchi bisa zarginsa da daɓawa dan uwansa wuka har lahira.

Leadership ta ruwaito cewa Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Ahmed Wakil Shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi a garin Bauchi.

Advertisement

Tsadar Rayuwa: An buga wawar buhunhunan kayan abinci a Kebbi

Ya ce an kama wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da jami’in ƴan sanda suka samu, inda nan take aka tura jami’an tsaro zuwa wurin da lamarin ya faru .

“Jami’ai Sun garzaya da wanda aka daɓawa sukar zuwa asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa Inda a nan ne likita ya tabbatar da mutuwar sa.

”Nan take jami’an tsaro suka fara farautar wanda ake zargin, inda aka yi nasarar kama shi a kusa da unguwar Kasuwan Shanu a cikin garin Bauchi.

Advertisement

“Binciken farko da ‘yan sandan suka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya yi amfani da wuƙa ne inda ya daɓawa kaninsa a ranar 31 ga Maris, 2024 biyo bayan wata yar gardama da ta kaure a tsakaninsu,” inji shi.

Wikki Time ta ruwaito cewa rikicin ya faro asali ne a lokacin da kanin ya bukaci yayan sa wato wanda aka kashe da ya daina shan sholi a Cikin ɗakin su saboda wari.Inda nan take rikici ya barke tsakanin su wanda ya kai ga kisa.

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply